Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya ce kasarsa za ta bayar da tallafin dala miliyan 600 ga kasashen Afirka domin su gudanar da ayyukan ci gaba.
Mr Modi ya bayyana haka ne a wajen taron da yake yi da shugabannin kasashen Afirka 50 a birnin Delhi.
Ana kallon wannan mataki a matsayin wani babban yunkuri da Indiya ke yi na jawo kasashen Afirka a jiki domin gudanar da harkokin kasuwanci.
Kasuwancin da ke tsakanin Indiya da Afirka ya ninka zuwa dala biliyan 72 tun daga shekarar 2007, sai dai ana ganin hakan ba shi da yawa.
Shugabannin da ke halartar taron na Indiya sun hada da: Muhammadu Buhari, Jacob Zuma, Robert Mugabe, AbdulFatah al-Sisi, Macky Sall da Omar al-Bashir.