Shin menene hukuncin kwanciyar ruf da ciki? Wato mutum ya kifa cikinsa ya kwanta. Naji wasu mutanen suna yin magana akan haka wai babu kyau. Shin wai Champi ne ko kuwa akwai wata hujjar da ta hana?
Bissalam, Tambaya daga Muhammad A. Nasir.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Kwanciyar Ruf da ciki, In dai ba bisa larura bane, To yin haka Makruhi ne bisa dokokin addinin Musulunci. Kuma tabbas akwai Hujjar Hadisi Sahihi daga Manzon Allah (saww).
Akwai hadisin da Imam Abu Dawud ya ruwaito daga Ya'eesh bn Tikhfah Alghifariy (ra) yace babansa yace :
"Watarana na kwanta akan ruwan cikina acikin Masallaci sai naji wani mutum ya girgizani da Qafarsa. yana cewa:
"ALLAH BA YA SON IRIN WANNAN KWANCIYAR".
Da na 'daga idona na duba sai naga ashe Manzon Allah ne (yayi min maganar) saww.
Kaga kenan wannan ya isa abinda Za'a kafa hujjah dashi akan Karhancin yin haka. Amma idan kana da larurar Ciwon baya, ko kuma wani rauni ko raunuka ajikinka, Kuma babu damar ka kwanta awani gefen jikinka, to babu laifi idan kayi ruf da ciki din.
WALLAHU A'ALAM.