TAMBAYA TA 1736
********************
ASSALAMU AlAIKUM MALLAM. Mallam ka taimaki rayuwana ina cikin wani halin tashin hankali, mallam akan tambaya da nayi kwanakin baya akan aure ne! Mallam mugun kokwanto ya shigeni. ko yaya nayi in kau da tunanin na kaasa.....Mallam na aikata zina shekaru biyar da suka wuce baya nan nayi wasan soyyaya da ba ta kai ga zina (romance) ba da samari kaman guda uku....na karshe da nayi a watan april ne sai nayi aure a june....
Mallam zuciya na nata raya mun abubuwa iri iri...kaman banyi istibrai ba saboda haka ba aure,chan kumma zuciya na na raya mun ban nemi tuba ba saboda hka ba aure...Mallam wanan tunanin ya sani cikin mugun tashin hankali wanda har ya kai ni ga gayawa miji na....mallam kullum in ina kwance da miji na sai zuciya na ya dinga raya ma cewa kwanciyar zina nikeyi.....
Mallam ka taimakeni da cikakkiyar bayani akan matsayin aure na saboda ina cikin tashin hankali
(Daga wata baiwar Allah)
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Mafiya yawan Malaman Musulunci sun tafi akan haramcin auren duk matar da kuma a taba aikata zina, Ko namijin da ya taba aikata zina, Har sai bayan sun tuba zuwa ga Allah (SWT) da cikakkiyar tuba irin wacce ALLAH din yake so.
Don haka in dai kin riga kinyi nadama kin zubda hawaye, kinyi itsighfari tare da kaurace ma Dukkan zina da dangoginta da kuma samarin da kike aikata zinar dasu, To aurenki yayi. Babu wata mushkila.
Maganar Istibra'i kuma, In dai kin riga kinyi Jinin haila sau daya, ko sau biyu ko uku kafin daurin auren, to shikenan ya zama shine Istibra'inki. Domin amfanin Istibra'i shine a kubutar da mahaifar Mace daga daukar Maniyyin Zina, Ko Juna biyu na zina zuwa ga gidan aure.
Kinga kenan aurenki ya yiwu babu wata mushkila tunda Zinar ta afku ne tun shekaru biyar da suka gabata.
Shi kuma wannan wasan da kikayi da wasu samari kafin aurenki ba Za'a daukeshi amatsayin abinda zai haramta yiwuwar wannan auren naki ba. Sai dai kuma yana daga cikin mafiya girman laifuffukan da Allah ya hanemu acikin littafinsa mai girma.
Allah yana cewa: "KADA KU KUSANCI ZINA. DOMIN ITA ZINA ALFASHA CE KUMA HANYARTA TA MUNANA".
Ya zama wajibi gareki ki maida hankali wajen gyara kusakuren da kika aikata a baya ta hanyar Komawa zuwa ga nan yardar Ubangijinki da yawan ayyukan alkhairi kamar su sadaka, kyauta, Sadar da Zumunci, Nafilfilin dare, Kyautata ma Mijinki, kyautata ma makobta, Kyautata ma iyayenki da nasa, Yawaita zikirin Allah da Karatun Alqur'ani, etc.
Bai kamata ki gaya ma mijinki wannan mummunan labarin ba. Tunda Allah ya riga ya rufa miki asiri bai kamata ki tona ma kanki ba. Wannan zai iya janyo miki lalacewar darajarki da mutuncinki agidan aurenki. Kuma Mijinki zai rika zarginki duk sanda kika fita unguwa.
Don haka kiji tsoron Allah ki kyautata tubanki awajen Allah azahiri da badini.
Allah yana cewa:
"YA KU BAYINA WADANDA SUKAYI 'BARNA BISA KAYUKANSU!! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA SAMUN RAHAMAR ALLAH. ALLAH YANA GAFARTA DUKKAN ZUNUBAI. SHI SHINE MAI GAFARA MAI JIN QAI".
Allah ya shiryeki damu baki daya.
WALLAHU A'ALAM.