TAMBAYA TA 1740
*********************
Assalamu alaikum, malam na kasance ina zuwa catering schl acikin wani coci amma bangaren da ake koyar damu bangare daban ne, yanzu haka na kammala koyon aikin saura graduation. Amma akwai Thanksgiving din da za,ayi a cikin main hall din (cikin cocin), kuma ance mana both Muslims suma sai sun halarta aciki.
To malam ina son sani shin idan mu musulman mun shiga akwai zunubi?.ko ya haramta agaremu sai mu bujure musu??
Daga yar'uwarku
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Akwai bambancin sa'banin ra'ayi atsakanin Maluman Mazhabobin Musulunci dangane da hukuncin shigar Musulmai cikin chochi.
Misali:
Mazhabin Hanafiyyah da Shafi'iyyah suna ganin cewa HARAMUN NE Musulmi ya shiga Chochi ko awanne dalili ne bai halatta ba awajensu. Sun kafa Hujjar cewa ai Shi chochi kamar gudan shaitanu ne. Tunda waje ne da ake yiwa Allah shirka. Kamar yadda Ibnu Nujaym Al-Hanafiy ya fada acikin littafin BAHRUR RAA'IQ Juzu'i na 7 shafi na 364. Da kuma Hashiyatu Ibni Aabideen juzu'i na biyu shafi na 43.
Amma su Shafi'iyyah sun takaita haramcin akan Chochin da yake Kunshe da Gunki ne. Amma idan babu gunki aciki to bai haramta ashiga ba. Kamar yadda yazo acikin wadannan manyan Litattafan Fiqhun Mazhabinsu:
* TUHFATUL MUHTAAJ. juzu'i na 2, shafi na 424.
* NIHAYATUL MUHJAAJ juzu'i na 2, shafi na 63.
* HASHIYAR QAYLUBIY juzu'i na 4 shafi na 236.
Su kuma Mazhabar Hanbaliyyah ta Imamu Ahmad bn Hanbal (rah) Suna ganin cewa MAKRUHI ne Musulmi ya shiga Chochin dake dauke da Gumaka. Amma idan babu Gumaka aciki to Bai zama Makruhi ba.
Haka Ibnu Taymiyyah ya fada acikin Fataawal Kubra juzu'i na 5 shafi na 327.
Su Hanbaliyyah sun kafa Hujjah ne da hadisin nan wanda Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yace:
"Manzon Allah (saww) yaga Gumaka acikin ka'abah din haka bai shiga Cikinta ba, har sai da yayi umurni aka kawar dasu tukunna".
(Sahihul Bukhariy hadisi na 3352).
Hakanan Akwai ruwaya daga Aslamu (wani bararren bawan Sayyiduna Umar ne). yace Lokacin da Sayyiduna Umar (ra) yaje Birnin Sham (Syria) wani babban Shugaban Kiristocin wajen ya shirya masa abinci acikin Chochinsu sannan yace masa yazo yaci.
Sai Umar yace masa "Ba zan shiga chochinku ba, saboda Gumakan da suke cikinsa".
(Aduba AL MUSANNAF na Imam ABDURRAZAQ juzu'i na 10 shafi na 398).
3. Wasu daga cikin Maluman Hanbaliyyah da kuma Malikiyyah har da Maluman Mazhabin Zahiriyyah suna ganin cewa YA HALATTA MUTUM MUSULMI YA SHIGA CHOCHI KODA AKWAI GUMAKAN ACIKI.
Sun kafa Hujjah da ruwayar da ta nuna cewa Sayyiduna Umar ya umurci AHLUL KITABI cewa su fadada wuraren ibadarsu saboda Musulmai su samu wajen kwana acikin tafiye-tafiyensu.
Hakanan acikin AL-MUGHNEE Ibnu Qudaamah ya kawo ruwayar nan wacce Ibnu A'iz ya kawo acikin Littafinsa FUTUHUSH SHAAM cewa Lokacin da aka gayyaci Sayyiduna Umar zuwa cin abinci a chochin nan, da bai je ba, Ya umurci Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) da sauran Sahabbai su sun shiga ciki har sunci abinci.
Don haka shigarki chochi bai haramta gareki ba, Mutukar dai babu wani abu na bautarsu mai cike da shirka wanda zasu gabatar alokacin.
Amma idan zasu sanya ku rera wakarsu ta shirka, ko su sanyaku rawa da Waqa, to bai halatta ku musulmai kuje ba.
WALLAHU A'ALAM.