Mr. Nick Dazan kakakin hukumar zabe INEC ya
bayyana cewa hukumar ta shirya ta gudanar da
zabukan jihohin Bayelsa da Kogi duk da cewa basu
da kwamishanoni kamar yadda da doka ta tanada
kuma wani fitaccen lauya ya jawo hankalin
hukumar kan lamarin
Shahararren lauya Mr. Femi
Falana yace hukumar zaben INEC bata da ikon
gudanar da zabukan a karkashin kundun tsarin
milkin kasar kasancewa kwamishanonin zabe
dake hedkwatar hukumar guda biyu ne kawai
maimakon akalla guda biyar.
Amma hukumar zaben bata yadda da matsayin
babban lauyan ba.Nick Dazan yace tun watan
shida na wannan shekarar suka fitar da jadawalin
zabukan lokacin da suke da kwamishanoni 13.
A cikin kundun tsarin mulki sashen da ya shafi
aikin hukumar ya ce idan an sami kwamishana
daya cikin uku ana iya gudanar da zabe.
Su ma jam'iyyun kasar sun shirya tsaf domin
tunkarar zaben. Maimala Boni sakataren
jam'iyyar APC na kasa yace suna da kwarin
gwuiwar lashe zabukan saboda mutanen dake
jihohin biyu sun kosa da halin da suke ciki yanzu.
Suna bukatar canji.
Shi ma gwamnan jihar Kogi Idris Wada ya karfafa
magoya bayansa saboda zasu sami nasara.
Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa
Barrister Abdullahi Jalo yace da yaddar Allah
jihohin biyu zasu cigaba da kasancewa hannun
PDP.
Title :
Hukumar Zabe INEC ta Shirya
Gudanar da Zabukan Jihohin Bayelsa
da Kogi
Description : Mr. Nick Dazan kakakin hukumar zabe INEC ya bayyana cewa hukumar ta shirya ta gudanar da zabukan jihohin Bayelsa da Kogi duk da cewa basu ...
Rating :
5