Jaridar SaharaReporters ta bayyana cewa, hukumar sojin Najeriya ta juma tana bincike shi saboda ko in kula daya ke nunawa wajen yakar Boko Haram. Hakan yayi sanadiyyar daya sanya yan Boko Haram suka amshe Baga, Ciyabar runduna to soji ta kasa da kasa.
Hukumar soji ta yanke mashi hukuncin wata 6 domin kin jajircewa da yayi. Sannan kuma ta kama shi da laifin kin kula da makaman da aka sanya a karkashin shi.
Birigediya Ransome-Kuti ya musanta zargin da ake yi mashi inda ya bayyana cewa ba laifin shi bane abubuwan da ake zargin shi dasu.
Lauyan Birigediya Ransome-Kuti, Femi Falana ya musanta zargin a kotun inda ya bada wasu shaidu masu nuna cewa hukumar Sojan me ta ki bada Kayan aiki inda yake kare Ransome-Kuti daga duka zargin da ake yi ma shi.