Hukumar bada lamani ta Duniya IMF ta shawarci
gwamnatin Najeriya, data sake duba dokokin data
kafa wanda ya shafi hada hadar kudaden
kasashen waje, hakan ne ma yasa masana da yan
kasuwa suka fara sharshi kan wannan shawara.
A sanarwar da wata jami’a a
hukumar ta IMF mai suna Antoinette Sayer ta
aikawa babban bankin Najeriya CBN, tace matakin
na kawo cikas ga hada hadar kasuwancin cikin
gida da na waje. Alhaji Kasimu Garba Kurfi shine
shugaban kamfanin hada hadar kudi a saka jari
na APT a birnin Lagos, wanda ya goyi bayan
matakin da IMF din ta dauka, inda yace bayadda
za’ayi ace Najeriya ta tsayar da farashin dala
kasancewar bata da wadatar dalar.
Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, ya
tambayi mukaddashin kungiyar masu hada hadar
kudaden kasashen waje na Najeriya Alhaji Aminu
Gwadabe, ko yaya masu hada hadar kudaden
kasashen wajen ke kallon matakin gwamnati da
kuma na IMF? Wanda ya bada amsa da cewa shi a
ganin shi wannan shawarar bata dace ba, saboda
IMF na tambayar Najeriya ne ta karyar da darajar
Naira da cewa sai anyi haka ne kasar zata zama
dai dai.
Ko a cikin wannan makon sai da gwamnan babban
bankin tarayyar Najeriya, ya jaddada cewa
gwamnati zata duba wannan tsari, domin
tallafawa bankuna da kuma ‘yan kasuwa.
Title :
Hukumar IMF Ta Shawarci Najeriya
Da Ta Karyar Da Darajar Naira
Description : Hukumar bada lamani ta Duniya IMF ta shawarci gwamnatin Najeriya, data sake duba dokokin data kafa wanda ya shafi hada hadar kudaden kasa...
Rating :
5