BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Salati da amincin Allah su tabbata ga Babban bawansa, wanda shine mabudin Aljannarsa, wato Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa masu alfarma, da Sahabbansa Madaukaka.
Idan Daliban ZAUREN FIQHU basu manta ba, awancan karatun mun tsaya ne akan bayanin hanya ta 12. Yanzu kuma in sha Allah zamu dora.
13. Hadisi ne daga Sayyiduna Rafi'u bn Khadeej (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"Idan dayanku ya kwanta bisa hakarkarinsa na dama, sannan yace:
"ALLAHUMMA ASLAMTU NAFSEE ILAIKA. WA WAJJAHTU WAJ-HEE ILAIKA. WA ALJA'ATU ZAHREE ILAIKA. WA FAWWADHTU AMREE ILAIKA. LAA MALJA'A WALA MANJA MINKA ILLA ILAIKA. UWMINU BIKITABIKA, WA BI RASULIKA".
To idan ya mutu acikin wannan daren zai shiga Aljannah.
(Tirmidhy ne ya ruwaito).
14. HADDACE SUNAYEN ALLAH:
Hadisi ne daga Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"HAKIKA ALLAH YANA DA SUNAYE GUDA CHASA'IN DA TARA. DARI NE BABU GUDA DAYA. DUK WANDA YA HADDACESU ZAI SHIGA ALJANNAH".
(Ibnu Maajah ne ya ruwaitoshi).
15. FA'DAR LA ILAHA ILLLAL LAHU :
Hadisi daga Abu Dharrin Al-Ghiffariy (ra) yace:
"Naje wajen Manzon Allah (saww) sai na tarar dashi yana barci alhali yana sanye da fararen tufafi. Sannan ya sake dawowa wajensa na tarar dai yana barci, Sannan na sake dawowa sai na tarar ya farka.
Da na zauna awajensa sai yace :
BABU WANI BAWA WANDA ZAI CE "LA ILAHA ILLAL LAHU, KUMA YA RASU BISA HAKAN FACHE SAI YA SHIGA ALJANNAH".
Sai nace "Koda yayi zina? Koda yayi sata?". Sai yace "EH KODA YAYI ZINA, KODA YAYI SATA".
Sai na sake cewa "Koda yayi zina, koda yayi sata?" Sai yace min "EH KODA YAYI ZINA, KODA YAYI SATA". Sai da mukayi haka sau uku.
A karo na hudu sai yace "KODA ABU DHARRIN BA YASO".
Sai Abu Dharrin din ya fito yana ceqa: "Koda Abu Dharrin ba yaso".
(Imamu Muslim ne ya ruwaito hadisin).
16. GAISAR DA MARAR LAFIYA :
Babu wani musulmin da zai je gaisar da marar lafiya da safe, fache sai Mala'iku dubu saba'in (70,000 ANGELS) sun rika yi masa Salati (wato addu'a) har zuwa yamma.
Idan kuma yaje ya gaisar dashi da yamma sai sun rika yi masa Salati har gari ya waye.
Kuma za'a bashi Dausayi daga Aljannah".
(Sahihut Targheeb).
17. DUBIYAR MARASSA LAFIYA :
Hadisi daga Thawbaan (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa :
"HAKIKA MUSULMI IDAN YAJE DUBIYAR 'DAN UWANSA MUSULMI, BA ZAI GUSHE ACIKIN YANKIN ALJANNAH BA, HAR SAI YA KOMO".
Sai Sahabbai suka ce "Ya Rasulallahi menene Yankin Aljannah?". Sai yace: "DAUSAYINTA".
(Muslim ne ya ruwaito).
18. TSAYAWA BISA GASKIYA KO YAUSHE:
Abu Mas'ud (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"NA HOREKU DA YIN GASKIYA. DOMIN ITA GASKIYA TANA SHIRYARWA ZUWA GA BIN ALLAH. SHI KUMA BIN ALLAH YANA SHIRYARWA ZUWA GA ALJANNAH.
MUTUM BA ZAI GUSHE YANA YIN GASKIYA BA, KUMA YANA KIRDADON INDA GASKIYAR TAKE, FACHE SAI AN RUBUTA AWAJEN ALLAH CEWA SHI MAI GASKIYA NE.
INA TSORATAR DAKU DAGA YIN QARYA. DOMIN ITA QARYA TANA SHIRYARWA ZUWA GA FAJIRCI. SHI KUMA FAJIRCI YANA KAIWA ZUWA GA WUTA.
MUTUM BA ZAI GUSHE YANA YIN QARYA BA, KUMA YANA KIRDADON INDA QARYAR TAKE, FACHE SAI AB RUBUTASHI AWAJEN ALLAH CEWA SHI MAKARYACI NE".
(Bukhary ne ya ruwaitoshi).
19. MUTUWA AWAJEN BAQUNTA:
Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru (ra) yace:
"Wani mutum ya rasu a Madinah daga cikin wadanda aka haifa acikinta. Sai Manzon Allah (saww) yace "YA KAICHONSA! INA MA DA YA MUTU AGARIN DA BA GARIN HAIHUWASA BA!!!".
Sai Sahabbai suka ce "Saboda menene haka Ya Rasulallah?".
Sai yace "HAKIKA SHI MUTUM IDAN YA MUTU AGARIN DA BA GARIN HAIHUWARSA BA, ZA'A KIYASTA MASA (NISAN) TUN DAGA GARIN HAIHUWARSA HAR ZUWA KARSHEN WAJEN DA YAKE ACIKIN GIDAN ALJANNAH"
(Nisa'iy ne ya ruwaito hadisin).
20. GYARAN HANYAR WUCEWAR MUSULMAI
Hadisi daga Abud Darda'i (rta) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA KAWAR DA WANI ABU WANDA YAKE CHUTAR DASU DAGA KAN HANYAR MUSULMAI, TO ALLAH ZAI RUBUTA MASA HASANAH GUDA DAYA. KUMA DUK WANDA ALLAH YA RUBUTA MASA HASANAH GUDA TO ZAI SHIGAR DASHI ALJANNAH".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
21. TSORON ALLAH DA KUMA KYAWUN HALAYE:
Daga Abu Hurairah (ra) yace "An tambayi Manzon Allah (saww) akan abinda yafi shigar da mutane Aljannah. Sai yace "TSORON ALLAH DA KUMA KYAWAWAN HALAYE".
Kuma an tambayeshi akan abinda yafi shigar da mutane WUTA. Sai yace "BAKI DA KUMA FARJI".
(Imam Tirmiziy ne ya ruwaito).
22. KALMOMI MASU DADI :
Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"HAKIKA BAWA WALLAHI ZAI IYA YIN MAGANA DA WATA KALMA TA YARDAR ALLAH, WACCE BAI BATA WANI MUHIMMANCI BA, AMMA SAI ALLAH YA DAUKAKASHI DA DARAJOJI ACIKIN ALJANNAH.
KUMA HAKIKA BAWA ZAI YI MAGANA DA WASU KALMOMI NA FUSHIN ALLAH, WANDA BAI BASU WANI MUHIMMANCI BA, AMMA AN DULILMIYAR DASHI ACIKIN JAHANNAMA SABODA ITA".
(Bukhary ne ya ruwaito).
Anan zamu tsaya, da fatan ALLAH yasa duk wanda ya karanta yayi amfani dashi. Allah ya Qara bunkasa ZAUREN FIQHU, ya saka ma dukan daliban da alkhairi