************************************************
Abubakrin Alqarashiy ya ruwaito tare da Isnadinsa zuwa Sayyiduna Abdullahi bn Umar bn Al-Khattab (rta) yace:
"Watarana Iblees (L.A) ya hadu da Annabi Musa (as) sai yace masa: "YA MUSA!!! Kai ne wanda Allah ya zabeka ya baka Manzancinsa, Kuma yayi Zance da kai. Ni kuwa ina daga cikin Halittun Allah ne. Nayi Zunubi kuma ina so in tuba. Ina so Ka nema min ceto awajen Ubangijinka mai girma da daukaka, Ya yafe min ya karbi Tuba na!!".
Shikenan sai Annabi Musa (as) ya daga hannayensa ya roki Allah. Nan take sai aka ce masa "YA MUSA, AN BIYA MAKA BUKATARKA".
Da Annabi Musa ya hadu da Iblees sai yace masa : "AN UMURCEKA KAJE KAYI SUJJADA GA QABARIN ANNABI ADAM (AS). SANNAN ZA'A KARBI TUBANKA".
Sai Iblees ransa ya 'baci, Yayi girman kai, yace : "BANYI MASA SUJJADAH TUN LOKACIN DA YAKE RAYE BA, DON ME ZANYI MASA SUJJADAH BAYAN YA RIGA YA MUTU!".
Yaci gaba da cewa: "Ya Musa lallai kana da hakki akaina saboda ceton nan da ka nema min awajen Allah. Don haka ka rika tunowa dani alokutan nan guda uku, Don kar ka hallaka acikinsu:
1. Ka rika tunowa dani aduk lokacin da kayi fushi. Domin wahayina yana shiga cikin Zuciyarka, Kuma Idanuna suna cikin Idanunka (alokacin fushi). Kuma ni ina yawo acikin Jikinka kamar yadda jinin jikinka yake yi.
2. Ka rika tunowa dani (wato sharri na) alokacin da zaka hadu da abokan gaba (awajen Jihadi). Domin ni ina zuwa ma 'Dan Adam aduk lokacin da zai hadu da kafirai awajen yaki, Ina tuno masa da 'Ya'yansa da Matarsa da Iyalansa, Har sai nasa ya juya baya (ya gudu daga wajen Yaqin).
3. Kar ka yarda ka zauna waje guda da Matar da ba muharramarka ba. Domin nine 'dan aikenta zuwa gareka, Kuma 'dan aikenka zuwa gareta". (Wato Zan chusa mata sha'awarka, kaima zan chusa maka sha'awarta).
(Aduba cikin AAKAMUL MARJAAN shafi na 207).
****************
DAGA ZAUREN FIQHU :
Ya Allah ka tsine ma Shaitan da Jama'arsa, Ka Qara nisantar dashi daga rahamarka. Ka kiyayemu daga sharrinsa da sharrin rundunoninsa La'anannu. Aaameeen.