Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda
gaba daya na gama tsinkewa da al'amarinta.
Laifinka ne Darling saboda na fada maka ba
zan iya rayuwa ba kai ba, na bukaci ka bari
mu ci gaba da waya kuma mu dinga
communicating a social network kamar da
amma ka ki, na yi iya kokarina in ga cewar
na fitar da kai cikin raina abu ya faskara. Ta
fada tana yi min fari da idanunta.
Amma kuma ai ya kamata ki san cewa cikin
fushin ubangiji ne kike son jefani, ta yaya zan
amince da wannan bukatar taki, kuma idan
ma ban ji tsoron Allah ba ai ko don gudun
azabar mijinki dole in kaurace maki. Na ce da
ita
Calm down mana yusuf in dai matsalar mijina
ce nayi maka alkawarin ba zai koma tabamin
kai ba. Tayi saurin katseni....
Wasa-wasa farida ta maida unguwarmu
kamar gidansu kusan kullum sai ta zo
wajena in bata zo gidanmu ba to zata sameni
shago kuma kullum ta zo zancen daya ne, ba
irin magiyar da ban yi mata ba akan ta daina
zuwa wajena, sai cewa tayi idan ina so ta
daina zuwa inda nake to in bari mu ci gaba
da hulda a social network kamar yanda muke
a da, tun abin baya damuna har ya fara
damuna ga mutanen unguwarmu sun fara
tsegumina,gidanmu kuwa mahaifiyata kullum
sai tayi min fada akan yawan zuwan da
farida ke yi nemana tun inai mata karyar dinki
ne ke kawota har ta daina yarda da karyar.
Da na fahimci ba zata daina zuwa ba tilas na
amince da bukatar....
BABBAN GANGANCINA KENAN DANAYI
ARAYUWA.
Amincewar da nayi wa farida muka ci gaba
da hulda a social network da kuma ta waya
kamar da, ya sa ta daina zuwa unguwarmu.
Ko da yaushe sai dai mu rika haduwa a
facebook, ko WhatsApp, ko kuma ta kirani a
waya. Haka Al'amarin ya ci gaba da
kasancewa har zuwa wasu 'yan kwanaki...
Yau ma kamar kullum zaune nake a kan
keken dinkina, ina dinki. Kamar daga sama
nagansu, sun fado cikin shagon, basu tsaya
cewa dani komai ba cakumoni kawai suka yi
suka yi waje dani suka yi jifa dani cikin
motarsu kirar Hilux, kamar fitar kibiya daga
kwari, haka suka figi motar suka yi gaba
dani. Yaran Kwamanda ne (Sojoji)
Tun cikin motar suka fara nukurkusata, koda
muka isa barikin tuni na fice daga hayyacina.
Koda hankalina ya dawo jikina, na ganni ne a
wani daki da zan iya kira da kurkuku mafi
kunci a duniya. Ba sai na tsaya wani bincike
ba na san Kwamanda ne ya sa aka kamoni
saboda kunnen uwar shegu da nayi da
gargadinsa.
Nadama ce ta zomin irin wacce ban taba
yinta a rayuwata ba tunanin wahalar da na
sha kwanakin baya a hannunsa ta ya zomin,
lokaci daya kuma tsanar farida ta shigeni
lokacin da na tuna da alkawarin da ta yi min
a farkon zuwanta shagon dinkina. Tabbas
farida annoba ce a rayuwata...
Karar bude dakin ce ta katseni daga tunanin
da nake yi lokaci daya tsoro ya dabaibayeni
na tsura wa kofar idanu, don ganin wa zai
shigo.
Kwamanda ne ya shigo. Sanye yake cikin
kaki (Uniform) ba kamar wancan karon ba,
kallo daya nayi wa fuskarsa na fahimci ransa
yayi mutukar baci.
Kunnen kashi ne da kai ko yaro? Ya jefamin
tambaya. Bai bani damar amsa masa
tambayarsa ba kai tsaye ya ci gaba da
magana.
Ko da yake laifina ne da na baka damar da
zaka bijirewa umarnina,
da na batar da kai tun a wancan lokacin da
tuni nayi maganin taurin kan nan naka.
Amma ko yanzu ban makara ba, ina da
damar yin hakan.
Ban ankara ba sai ganinsa nayi rike da
bindiga yana kokarin saita kokon kaina.
Saboda firgici ban san lokacin da fitsari ya
kubucemin a wando ba,..nan danan nahau addu'an daduk tafadomin
abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji saukan bindigar akaina
amma shiru