Farida taci gabada cewa, Ba karamar
barazana na fuskanta ba Saboda na san ba
abu ne mai yiwuwa ba nayi soyayya da kai
alhalin da aure a kaina,
Wannan ya sa na shiga tunanin mafita, daga
baya na yanke shawarar na boye maka ina
da aure.
Idan har ba yaudarata kike yi ba maganar da
kika fada gaskiya ne ya akayi Kwamanda ya
san muna tare?
Akasi aka samu nayi rashin lafiya ne mai
tsanani wacce ta kaini ga kwanciya asibiti,
bana raba daya biyu WhatsApp dina ya shiga
yai min bincike anan yaga Chat dina da kai,
kuma har kaje gidan ka dawo ban san an yi
ba ina Asibiti.
To ya aka yi kika sani? Bayan kin ce ba ki
gidan.
Shi ne ya sanar dani bayan naji sauki.
To wane mataki ya dauka a kanki?
Hmm! Yusuf kenan, idan akwai abinda
Kwamanda ya tsana a rayuwarsa to bacin
raina ne, shi yasa duk abinda nayi bayamin
fada bare har ya dau wani mataki a kaina.
To yanzu me kika zo yi wurina? Kuma me
kike so in yi maki?
Hakuri na zo baka, a kan abinda yai maka,
sannan kuma naga kayi blocking dina a
facebook da WhatsApp shi ne na so jin dalilin
hakan?
Zancen Hakuri nayi, zancen Blocking kuma
saboda ba zai yiwu in ci gaba da soyyaya da
matar aure ba, a matan auren ma kuma
matar soja. Sojan ma kwamanda
Ba soyayya zamu ci gaba da yi ba yusuf,
kawai gaisawa zamu rika yi kuma ka ci gaba
da turomin Labarai. Ta fada tana yi min wani
kallo, wanda ni a ganina na yaudara ne.
Ba zai yiwu ba farida, zai fi kyau ki kama
gabanki kar ki sake jefani a wata musibar.
Ka gasgatani yusuf nayi maka Alkawarin
babu abinda zai sameka wancan karon ma
akasi aka samu. Tace dani
Na fada maki fa ba zai yiwu ba, ki sani ko
wannan hirar da muke yanzu zunubi ne muke
kwasa saboda haka kawai ki kyaleni kar ki
sani fadawa cikin fushin ubangiji.
Ba irin magiyar da bata yi ba, amma naki
amincewa, dole ta hakura.
Da zata tafi kudi ta dauko daga jakarta
wadanda ba xan iya cewa ga adadinsu ba,
amma a kiyasin da nayi kudade ne masu
tarin yawa ta ajiye a kan telata,
Na meye? Na tambayeta.
Baka nayi, na san ba zaka rasa 'yan
hidindimu a gabanka ba. Tace dani tana
kokarin fita.
Kuma sai na ce dake bani da kudin da zan yi
hidindimun nawa ko? Kar ki mayar dani wata
haja mana, wacce zaki rika saye da kudi a
duk lokacin da kika ga dama. Na fada a
fusace.
Kayi hakuri ba nufi na ba kenan, gani nayi ba
komai ba ne don na baka kyauta, amma
tunda kayi min wata fassara, shi kenan ba
zan kara ba.
Zai fi kyau hakan, nace da ita ina kokarin
mika mata kudin.
Na dauka ta hakura kamar yanda ta nuna
ashe tana kasa tana dabo, gwara ma a ce na
amince da bukatarta a kan abinda ya biyo
baya
HAKAN SHINE BABBAN KUSKURENA DAYAFI
NABAYA..
Hankalina ba karamar kwanciya yayi ba
ganin cewa na yadda kwallon manguro zan
huta da kuda.
Bayan kamar kwana biyar da zuwan farida
shagon da nake dinki. Da sassafe ina
kwance dakina dake kofar gidanmu na ji
kanina Hafizu yana kwankwasamin kofa,
koda na bude yake shaidamin wai nayi
bakuwa tana nan kofar gida tana jira.
Kaina ba karamar daurewa yayi ba jin cewa
wata ta zo nemana har gida domin kuwa
wannan shi ne karo na farko da mace ta taba
zuwa nemana a gida. Duk matan da nake yi
wa dinki sai dai su zo nemana a shago kuma
ko basu sameni ba Aminu wanda muke dinki
tare zai kirani a waya in zo.
Cike da mamaki na fito daga dakin na nufi
kofar gidanmu, tun daga nesa na hango
mota tsugunne a kofar gidan, bana raba
daya biyu motar farida'ce gabana ya bada
rass!
Kamar in juya sai dai na daure na isa. Ta
bude kofar sashen mai tuki ta zuro kafafunta
waje sanye cikin jan material rike da waya
kirar Sony Ericson Xperia tana chating.
Farida ce.
Murmushi ta jefeni da shi yayin da ni kuma
na daure fuska tare da jeho mata tambaya.
Me kika zo yi a gidanmu?
Wurinka na zo yusuf ta fada tana kokarin
mikewa tsaye.
Haba! Farida yanzu kina ganin ya dace a
matsayinki na matar aure ki rika zuwa
wajena, kuma baki tunanin zuwanki gidanmu
zai iya haifarmin da matsala wajen iyayena?
kuma kin san mijinki yai min tsakani da ke.
Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda
gaba daya na gama tsinkewa da al'amarinta...