Kamshin turaren da ya gauraye madaidacin
shagon shi ya kara tabbatarmin da
shigowarta ciki,
gabana sai tsananta bugawa yake kara yi,
tunanin masifar da zan sake shiga ya sani
tsurewa.
Sallamar da tayi min ce ta sa ba shiri na
daidaita kaina nayi kokarin boye fargabar da
ke kokarin bayyana a fuskata.
Sannunka Tela, tace dani.
Yauwa sannunki, na amsa mata.
Dinki nake so kayimin, ta gabatarmin da
bukatarta
Ga shi kuwa kin zo a makare. Na fada cikin
gatse.
Murmushi tayi sannan tace wane irin makare
sai kace wacce ta kawo dinki daren Sallah
kuma tace yanzu take son a dinke mata.
Ba wannan makarar kika yi ba Hajiya, ina
nufin kin zo a lokacin da na daina yi wa mata
dinki, na fadi haka ne saboda tsayuwarta
cikin shagon ta fara gundirata kuma a koda
yaushe gani nake Kwamanda zai iya fadowa
cikin shagon.
Maganar da na fada maimakon tayi
sanadiyar barinta shagon, ga mamakina sai
gani nayi ta nemi kujera ta zauna.
Dan rainin hankali shi ne ka wani shareni
kamar baka ganeni ba, to wurinka na zo
magana nake so muyi, ta fada tana kokarin
kakaro murmushi.
A ina kuma kika san wannan sunan nawa?
Na tambayeta
Wane suna kake magana? Ta tambayeni ita
ma.
Dan rainin hankali mana. Na fada mata
Dariya tayi har sai da kyawawan hakoranta
suka bayyana.
Au! Dama sunanka ne kenan?
Kai dai ko yaushe baka rabo da abin dariya.
Na gode amma zai fi kyau kiyimin bayanin ko
ke wace ce? Na fada ina kokarin rufe babin
wasar da take kokarin budewa.
Na san ka san ko ni wace ce, amma tunda ka
nuna baka sani ba zan kara sanar da kai,
farida ce. Kona ce faridarka ce Ta sanar dani.
Wace farida kenan? Na sake tambayarta.
Haba my one kar ka mun haka please, yanzu
ashe duk soyayyar da kake nunamin a waya
yaudara ce ba sona kake yi ba? Ta fada cikin
murya mai rauni.
Look! Farida ba fa zan yarda ki sake jefani a
wani bala'i ba, ba ni kadai ne saurayi a garin
nan ba, zai fi kyau ki je ki nemi wani ki kara
yaudararsa ni wacce kika yimin ta isa haka.
Ka tsaya ka fahimceni yusuf ba wata yaudara
tsakaninmu. Ta fada tana kokarin
tabbatarmin da abinda ta fada har cikin
zuciyarta ne.
Dago fuskata nayi na kalli fuskarta ga
mamakina hawaye na gani suna sartu a kan
kyawawan kumatunta.
Hawayen sun karayar dani amma sai na
dake.
Farida kenan, abinda baki fahimta ba shine
an dade ana ruwa kasa na shanyewa.
Kalamanki na yaudara ba zasu kara tasiri a
gareni ba.
Yanzu ke ko kunya ba zaki ji ba da aure a
kanki ki rika bibiyar samari kina jaza musu
fitina?
Ka daure ka saurareni yusuf Wallahi gaskiya
zan fada maka. Tace dani
Ina jinki.
Tasowa tayi daga inda take zaune tazo dab
da telata, kusancin dake tsakaninmu har sai
da na rika jin bugun numfashinta.
Ka kalli kwayar idona ka fadamin idan ka ga
yaudara a ciki. Ta bukaceni.
Idan kin manta akwai bukatar na tunatar
dake cewa ke matar aure ce fa, saboda haka
kawai ki fadamin abinda kike son fadamin ina
saurarenki.
Kayi hakuri da masifar da na jefaka, da kuma
boye makan da nayi cewa ni matar aure ce,
ban yi haka don in cutar da kai ba, nayi ne
saboda na san idan har na sanar da kai ni
matar aure ce ba zaka kulani ba.
Kuma ban san mijina ya dakeka ba sai daga
baya, da ba yanda za'a yi na bari hakan ta
faru, na san babu yanda za'a ka yarda da
zancena idan har ban sanar da kai ko ni
wace ce ba.
Ina jinki.... Nace da ita saboda kalaman nata
na yaudara sun fara isata.
Kwamanda bai maka karya ba ni matarsa ce,
amma ba na sonsa ba kuma da son raina na
aureshi ba, iyayena ne suka auramin shi
saboda la'akari da mukaminsa da kuma
dukiyar da yake da ita, basu yi la'akari da
cewar bana sonsa ba, kuma me zai je ya
dawo bayan auren.
Me yasa bakya sonsa? Na katseta da
tambayata.
Baka bukatar dogon bayani yusuf, ba sai na
fada ba kai kanka kasan kyakkyawa kamata
bata dace da tsoho mai tarin shekaru irin na
Kwamanda ba.
Na tsinci kaina a cikin kunci bayan tarewata
a gidan Kwamanda, ba wai ya gaza wajen
bani jin dadin duniya ba ne, ko daya, kawai
dai na tsaneshi ne,
wannan ne yasa ni fadawa a social network
ko zan hadu da kawaye masu debemin kewa.
Lokacin da na fara facebook shafukan bayar
da dariya da saka nishadi nayi ta nema ina
shigarsu, a garin lalubena ne na ci karo da
kai wata kawa nane taban labarin indai labari
nakeso na nemi Magana Jari nasha labari,
Kuncin da nake fama da shi ya ragu, saboda
labaran da nake karantawa a wadannan
shafukan, sai dai duk cikin shafukan ba
kamar naka domin kai gwanine. Kai
DAN'ZAKI NE wane yaro
Lokacin da na fara cin karo da lambarka ta
WhatsApp ba karamin farin ciki nayi ba
saboda naga hanya mafi sauki da zan rika
samun labaranka.
Yawan karanta labaranka da nake yi, sai naji
ka fara birgeni, sannu a hankali sai naji na
kamu da sonka.
Ba karamar barazana na fuskanta ba Sabod a
na san ba abu ne mai yiwuwa ba nayi
soyayya da kai alhalin da aure a kaina,