Kai tsaye kwamanda ya nemi kujera
yazauna. ci gaba da maganarsa, ban yi
tunanin zaka shigo hannuna da wuri haka
ba,
koda yake kuma ba abin mamaki ba ne
domin kuwa Hausawa sun ce kuda wurin
kwadayi ake mutuwa, to kai a kudan ma ka
zarta kowa a kwadayi.
Na rasa gano me ke damunku 'ya'yan
talakawan nan ba zaku iya tsayawa a
matsayinku ba ku nemi 'ya'yan talakawa
tsaranku, sai kullum ku ne like da kyawawan
mata, matan da aka yi don masu hannu da
shuni in ban da wauta irin taku talakawae zai
kai ku wurin.
Ba sai na tambayeka ba dan samari ga
mamaki nan karara a fuskarka, na san kana
mamaki ne jin na ce maka farida matata ce, a
farko kuma na ce maka 'yata ce ban maka
karya ba dan samari a tarin shekaru na haifi
farida, sai dai a zamantakewa ta aure matata
ce, na san ba yanda za'a yi ta sanar da kai
tana da aure ahi yasa nima na ce da kai ni ne
mahaifinta saboda na san zaka fi saurin
shigowa hannu, yanayin wahalar da nake ciki
bai hanani gano dogon mutumin dake tsaye
gabana mai wakiltar sunan kwamanda,,,,
Allah yayi masa baiwar tarin surutu kamar
waziri Aku ba.
Ba tare da la'akari da me zan ce ba ya sake
dorawa, babu abinda nake so a duniyar nan
kamar matata farida, idan kuma akwai
abinda na tsana a duniyar nan to abinda zai
rabani da ita ne.
gashi kai kana kokarin ka kwaceta daga
gareni.
Don girman Allah kayi hakuri, Wallahi ban san
matarka ba ce, hasalima ban san tana da
aure ba Wallahi da ko kusa ba zan nemeta
ba. Na tari numfashinsa ina masa magiya.
Murmushi Mugunta yayi min, sannan ya sake
ci gaba da maganarsa kwantar da
hankalinka ai na san baka san matata ba ce
da ba zaka yi gangancin zuwa gidan nan ba
domin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne.
Sai dai rashin sa'a daya kayi, ba na iya
yafewa duk wanda ya rabi farida da sunan
so, to kai gashi har soyayyar kuke yi.
Lokaci daya kuma sai ya turbune fuska
kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar
faridar, sannan ya kira Samudawan nan da
suka jibgeni dazu.
Ku mikaminshi wurin M.P (Military Police) a
yi masa horo mai tsanani har sai na
waiwayeshi.
Hankalina in yayi dubu a lokacin sai da ya
tashi jin Kwamanda ya bada umarnin a kai ni
wurin masu ladaftar da sojoji idan suka yi
laifi wato Military Police, ihu na shiga yi ina
masa magiya a kan yayi hakuri amma kamar
baya jina.
Wasa farin girki dukan da na sha a baya ba
ko duka ba ne yanzu zan fara shan azaba
Cakumata suka yi kamar tsumma suka yi
waje, muna tafe ina sake-sake a raina ko
shakka babu da za'a yi nadin sarkin wawaye
to babu wanda ya dace a nada sai ni.
Yaya daga haduwa da yarinya WhatsApp
muna soyayya ban taba ganinta a zahiri ba
haka ita ma bata taba ganina a zahiri ba sai
dai a hoto, kawai wani ya kirani a waya wai
mahaifinta ne yana son ganina sai kawai in
tashi in tafi, in ma har da gaske ne ai ita ya
kamata ta sanar dani sakon na mahaifinta
ba wai shi ya kirani ba, a gefe daya kuma ina
tunanin irin azabar da zan sha a hannun
M.P.
maganar wani abokina da ya taba zuwa
tirenin din soja ta fadomin wai ko soja yayi
laifi yana tsoron M.P su kamashi soboda
azabar da zai sha a hannunsu. soja kenan,
to ina ga ni farar hula, a farar hular ma zan fi
dacewa da a kirani da mace mai tsohon ciki
wata tara, a kan a kirani namiji saboda
ragwancina.
Da wadannan sake-saken muka isa suka
hannuntani a hannunsu suka kama gabansu.
Tashin hankali ba'a sa maka rana kwanana
biyu cur a hannun M.P suna ganamim azaba
har sai da na rika tunanin anya ba mutuwa
ne nayi ba, a lahira ne nake shan wannan
azabar, saboda kwata- kwata azabar bata yi
kama da ta matambayan duniya ba.
A washe garin kwana na uku kwamanda ya
bada umarni a sakeni bayan ya gargadeni a
kan ko mai sunan farida na kara kulawa na
san sauran..
Satina uku cur a gida ina jinyar raunukan da
M.P suka yimin ko kofar gida bana iya fita.
ina kwance ina jinya na toshe duk wata kafa
da nake ganin zan iya tuna farida nayi
blocking dinta a facebook da WhatsApp, na
goge lambobin wayarta da duk wasu hotuna
da ta turomin nata. ina ganin mun yi
bankwana kenan har abada, ashe wai da
sauran rina a kaba
.
Bayan kamar wata daya da gama jinyata, ina
zaune shago bisa keken dinkina na dukufa
sai dinki nake wata madaidaiciyar mota
launin ruwan siminti ta yada zango bakin
kofar shagon dinkin, wani abokina ya taba
fadamin sunan motar wai ko Continue
Discussion ne sunanta. Irinta ne mijin
kanwana hauwa.u jidda yake shiga
Gabana ba karamar faduwa yayi ba lokacin
da naga wata matashiyar budurwa ta fito
daga motar kai tsaye ta kunno kai cikin
shagon doguwa ce sai dai ba sosai ba tana
da matsakaiciyar fuska mai dan tsawo dauke
da dara-daran idanu da matsakaicin baki
tana da saje a fuskarta launin fatarta kuwa
wankan tarwada ce, shekarunta zasu iya
kaiwa ashirin da uku zuwa da biyar, kallo
daya nayi mata na shaidata kasancewar na
saba ganin hotunanta.
Farida ce.
me kuma ta zo yi a shagona? tambayar da
nayi wa kaina kenan...xakasanine..? Inka qara komawa chan..!