Karar shigowan sakon Whatsapp a wayata ne
ya farkar dani daga baccin da ya fara
daukata a kan keken dinkina. Kamar ba zan
duba wayar ba, saboda idan da sabo na
saba. kulli yaumin sakunan WhatsApp din
basa rabo da zarya a wayata na mutane
dabam-
dabam a sassan kasar nan masu bibiyar
labaraina a facebook......
Idan na ce biye musu zanyi, ba barina zasu yi
neman abin sawa a bakina ba, shi yasa a
duk lokacin da nake a shagon dinkin bana
kula sakunan.
Amma ga mamakina yau sai naji ina bukatar
duba wayar in ga sakon waye ya shigo.
Kamar kullum yau ma bakuwar lamba naci
karo da ita da gajeren sakonta na sallama.
Kamar ba zan amsa ba sai dai na daure na
mayar da martanin sallamar. Wanda wanna
shine farkon sanadin jefa kaina cikin wani
mummunar hadari mtws dana sani keyace...
Sakon lambar ya ci gaba da shigowa
Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ko?
Eh! Da wa nake magana? Na bada amsa tare
da yin tawa tambayar.
Farida, daya daga cikin fans dinka a Dandalin
facebook, aka bani amsa, naga wani post da
kayi kwanakin baya, naji dadin post din shi
yasa nace bari nayi adding dinka nan in nuna
maka jin dadina.
Allah Sarki! Wane post kenan? Na sake
tambayarta.
Post din Hasashe game da matsalolin maza,
gaskiya naji dadin post din sosai, ta bani
amsa.
Na gode, kuma da yardar Allah zan ci gaba
da yin wasu post din wadanda suka fi
wannan dadi.
Allah ko? Gaskia ko yusuf idan ka ci gaba da
nishandantar dani zan ji dadi sosai, saboda
zaka sa in manta da bakin cikin da ke
damuwata.
Ke kuwa wane bakin ciki ne wannan? Na jefa
mata tambaya cikin zakuwa da son jin
damuwarta.
Murmushi tayi gami da cewa kar ka damu
idan lokaci yayi zaka sani.
Ba zan iya tantance dogon lokacin da na
dauka ina hira da baiwar Allar nan ba, abinda
kawai na sani a ranar bata barni nayi dinki
ba har lokacin barina shagon yayi.
Tunda daga wannan lokacin shakuwa mai
karfi ta kullu tsakaninmu da farida, duk yanda
zanyi in samo labarin da zan tura mata
wanda zai sakata nishadi sai nayi.
Wani lokacin idan labaran suka kakare min
sai naji kamar na koyi halin hankakar da
wasu ke yi a duniyar fesbuk akan labaran
mutane, sai kuma in tuna da yanda zuciyata
ke tafasa a duk lokacin da naga wani ya
satar min labari ya mayar da shi na sa, dole
sai in fasa.
Ranar da duk kuwa ban yi postin labari ba ko
na tura mata a WhatsApp ba ranar zan sha
kiran wayarta, a duk lokacin da ta kirani na
kan samu karyar da nayi mata.
A irin haka ne wata rana labaran suka kakare
min, duk wata kafa da nake tunanin samun
labari ta toshe na samu kusan kwana uku ba
wani labari, sai ga kiran mutuniyar, bayan
mun gaisa, ta fara aikinta wato tambayata a
kan na daina nishadantar da ita, rasa karyar
da zan yi mata nayi saboda ban son fada
mata cewa labaran ne babu, karya nayi mata
cewa bani da data ne a wayata Suscribtion
dina ya kare.
Har ga Allah na yi mata wannan karyar ne
saboda bana tunani mace zata iya tura wa
namiji kati babu wata alaka ta jini a
tsakaninsu, amma ga mamakina bayan mun
gama waya da ita kawai sai ga sakonta na
tes ya shigo, ina dubawa lambobin kati na
gani kasansu kuma tayi rubutu kamar haka:-
yusuf ga kati nan kayi maleji dashi 1500 ne
ba yawa.
Ina gama karantawa kiranta nayi, tana
dagawa nace Haba! Farida ya zaki min haka?
Gaskiyi ki bar katinki bana so, ina da kudi
zan saya da kaina.
Nayi juyin duniyar nan akan ta
barshi ta kiya, da taga na matsa sai cemin
tayi sai dai idan ban so kar in loda in bai wa
wani don ita ta riga ta bani kuma na raina
kyautarta ne shi yasa na ce ba na so, kuma
ta gode. Da naga ta hasala dole na dawo
bata hakuri, da kyar ta sauko, sannan nayi
mata godiya na kashe wayata. Ai kuwa tun
daga ranar kati ya daina katsewa a wayata.
Idan har bani da kudi a wayar a kalla ka
sameni da naira dubu ciki, ba kuma ni nake
saya da kaina ba ita ce da take turomin.
DANA SANI KEYACE.
Wannan dalilin jefa kaina cikin wahala na
yanka kazan wahala ma kaina kumana fige
naci karoda wani babban dutsen daya fasan
zuciya asanadin farida....
Wannan fa..?