Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda
gaba daya na gama tsinkewa da al'amarinta.
Laifinka ne Darling saboda na fada maka ba
zan iya rayuwa ba kai ba, na bukaci ka bari
mu ci gaba da waya kuma mu dinga
communicating a social network kamar da
amma ka ki, na yi iya kokarina in ga cewar
na fitar da kai cikin raina abu ya faskara. Ta
fada tana yi min fari da idanunta.
Amma kuma ai ya kamata ki san cewa cikin
fushin ubangiji ne kike son jefani, ta yaya zan
amince da wannan bukatar taki, kuma idan
ma ban ji tsoron Allah ba ai ko don gudun
azabar mijinki dole in kaurace maki. Na ce da
ita
Calm down mana yusuf in dai matsalar mijina
ce nayi maka alkawarin ba zai koma tabamin
kai ba. Tayi saurin katseni....
Wasa-wasa farida ta maida unguwarmu
kamar gidansu kusan kullum sai ta zo
wajena in bata zo gidanmu ba to zata sameni
shago kuma kullum ta zo zancen daya ne, ba
irin magiyar da ban yi mata ba akan ta daina
zuwa wajena, sai cewa tayi idan ina so ta
daina zuwa inda nake to in bari mu ci gaba
da hulda a social network kamar yanda muke
a da, tun abin baya damuna har ya fara
damuna ga mutanen unguwarmu sun fara
tsegumina,gidanmu kuwa mahaifiyata kullum
sai tayi min fada akan yawan zuwan da
farida ke yi nemana tun inai mata karyar dinki
ne ke kawota har ta daina yarda da karyar.
Da na fahimci ba zata daina zuwa ba tilas na
amince da bukatar....
BABBAN GANGANCINA KENAN DANAYI
ARAYUWA.
Amincewar da nayi wa farida muka ci gaba
da hulda a social network da kuma ta waya
kamar da, ya sa ta daina zuwa unguwarmu.
Ko da yaushe sai dai mu rika haduwa a
facebook, ko WhatsApp, ko kuma ta kirani a
waya. Haka Al'amarin ya ci gaba da
kasancewa har zuwa wasu 'yan kwanaki...
Yau ma kamar kullum zaune nake a kan
keken dinkina, ina dinki. Kamar daga sama
nagansu, sun fado cikin shagon, basu tsaya
cewa dani komai ba cakumoni kawai suka yi
suka yi waje dani suka yi jifa dani cikin
motarsu kirar Hilux, kamar fitar kibiya daga
kwari, haka suka figi motar suka yi gaba
dani. Yaran Kwamanda ne (Sojoji)
Tun cikin motar suka fara nukurkusata, koda
muka isa barikin tuni na fice daga hayyacina.
Koda hankalina ya dawo jikina, na ganni ne a
wani daki da zan iya kira da kurkuku mafi
kunci a duniya. Ba sai na tsaya wani bincike
ba na san Kwamanda ne ya sa aka kamoni
saboda kunnen uwar shegu da nayi da
gargadinsa.
Nadama ce ta zomin irin wacce ban taba
yinta a rayuwata ba tunanin wahalar da na
sha kwanakin baya a hannunsa ta ya zomin,
lokaci daya kuma tsanar farida ta shigeni
lokacin da na tuna da alkawarin da ta yi min
a farkon zuwanta shagon dinkina. Tabbas
farida annoba ce a rayuwata...
Karar bude dakin ce ta katseni daga tunanin
da nake yi lokaci daya tsoro ya dabaibayeni
na tsura wa kofar idanu, don ganin wa zai
shigo.
Kwamanda ne ya shigo. Sanye yake cikin
kaki (Uniform) ba kamar wancan karon ba,
kallo daya nayi wa fuskarsa na fahimci ransa
yayi mutukar baci.
Kunnen kashi ne da kai ko yaro? Ya jefamin
tambaya. Bai bani damar amsa masa
tambayarsa ba kai tsaye ya ci gaba da
magana.
Ko da yake laifina ne da na baka damar da
zaka bijirewa umarnina,
da na batar da kai tun a wancan lokacin da
tuni nayi maganin taurin kan nan naka.
Amma ko yanzu ban makara ba, ina da
damar yin hakan.
Ban ankara ba sai ganinsa nayi rike da
bindiga yana kokarin saita kokon kaina.
Saboda firgici ban san lokacin da fitsari ya
kubucemin a wando ba,..nan danan nahau addu'an daduk tafadomin abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji saukan bindigar akaina amma shiru karshen labarin
na rufe idanuna ina jiran saukar harsashe a kokon
kaina.
Na share akalla mintina uku ina jiran saukar
harsashi a kokon kaina. Shirun da na ji ce ta sani
bude idanuna. Ganinsa nayi ya ajiye bindigar ya
samu wuri ya zauna sai faman huci yake kamar
wata kasa.
Ko me ya hanashi harbe kokon kan nawa? Kamar
yanda yayi ikirari.
Kamar ya san amsar da nake bukata, sai kawai ya
fara amsamin.
Kaci sa'a, ko kuma in ce Allah Ya yi lokacin
mutuwar bai yi ba, shi yasa naji tausayinka.
Wannan shi ne karo na farko da na saita bindigata
akan wani mutun, da nufin harbinsa, kuma ban
harbeshi ba.
Saboda haka yanzu zan maka Adalci daya.
Wancan karon na yi maka hukunci da laifin
GANGANCI, alhalin baka yi GANGANCIN ba.
TSAUTSAYI ne yasa ka yin laifin, yanzu kuma kayi
min GANGANCI, hukuncin ganganci ne ya kamata
in zartar a kanka,
amma ba zan yi hakan ba, zan yi maka rangwame,
in yima hukunci da wancan laifinka na TSAUTSAYI.
Zan karya hannuwan nan naka biyu, wadanda kake
amfani da su kana chatin da matan mutane.
Sojoji biyu ya kira daga waje ya basu umurnin
karya hannuwa duka biyun sannan ya ficewarsa.
Ina ji, ina gani suka rika kokowa da hunnuwana
kamar masu kokowa da icce har sai da suka
kakkaryani, saboda zafin ciwo ban san lokacin da
na some ba.
Lokacin da na farka, cikin shagon dinkina na ganni
mutane sun kewayeni, bayan sun tambayeni inda
ke min ciwo nayi musu bayani wuraren da na
karye. Suka kwasheni sai wurin mai dori aka
doramin hannuwan nawa sannan suka dawo dani
gida domin jinya..
yadda kuka Nayi zaton tunda kwamanda yasa
anmun hukunci na karshe shikenan na huta. Ashe
akwai abunda yafi hukuncin kwamanda zafi.
Kaikanka me karatu dakasha mamakin abunda
nagani. Zuciyana ta kone hanjin cikina yakada
domin abunda kunnuwa suke jiyemun nayi kukan
nadama awannar ranar. Nakwana da mamakin
halin mata. Ashe dama haka mace take da sharri?
Nida abokaina 'yan,uwana munsha mamakin
abunda muka gani. Barida nabaku labarin kawai
GAYADDA ABUN YAKASANCE
Washe gari ina kwance cikin gidanmu, abokina
waziri aku ya zo dubina, muna hira. Gefena kuma
'yar autar dakinmu ne. Hauwa'u jidda. Tayimun
kirki sosai na kayan cikin saniya. Zaune take tana
zubar da hawaye domin tausayin datake gwadawa
akaina kasancewar itane kaf dakinmu allah ya
hada jinana danata. Samada sauran 'yan.uwana
sai ga sakon farida ya shigo wayata na ce da
waziri aku ya karantamin sakon kasancewar bani
da hannuwan rike wayar bare ina karantashi da
kaina. Ga sakon kamar haka..
"Gareki Wawiyar zuciya mai cike da kwadayi, ka
bani mamaki yusuf domin kuwa ban zaci zan yi
nasara a wannan wasan da sauki haka ba.
Na zaci wasan zai yimin wahala ganin cewar da
gwani ne zan yi wasar, sai gashi na sami akasin
hakan, ashe hangen kitse ne nake yi wa rogo, a
yanda nake ganin rubuce-rubucenka na dauka kai
gwani ne a wannan wasan ashe wai baka ma san
yanda a ke buga wasan ba.
Na san zaka bukaci sanin dalilin buga wasan, to
zahirin gaskia lokacin da na fara karo da
labaranka, haka kawai na ji na tsaneka, na dade
ina nazarin dalilin da yasa na tsaneka, sai daga
baya na fahimci ba komai ne ya sa ni tsanarka ba
sai ganin cewa kai ba wani marubuci ba,
amma ka dage, wai kai sai kayi rubutu kuma wani
abin karin haushi duk rubuce-rubucenka su kan
kare ne a wance ta yaudareka, wance ta ci
amanarka, wance kuma tayi maka wulakanci,
zancen duk daya ne.
Shi yasa na ga ya kamata idan duk wadancan da
kake fada sharri ne kake musu, to ni bari in yi
maka na gaskiya sai kayi mai dalili
Da nayi niyyar kyaleka a dukan farko da mijina yai
maka sai kuma naga ai baka doku ba tunda gashi
baka daina abinda kake yi a da ba, don haka sai
na ga wancan wasan first half ne muka buga ya
kamata a ce mun buga second half.
Yanzu kam wasa ya kare tunda nayi nasara. Kar
ka manta da ni domin kuwa nima ba zan manta da
kai ba. Hawayene ke zuba idon domin jin wannan
mummunar sakon na farida nasha mamaki nayi
zaton sone na gaskiya ashe cutane dama
Tabbas wannan mata ta kai Azzaluma nq fada a
raina
Bata yi kuskure ba da ta kira zuciyata da wawiyar
zuciya kuma mai kwadayi, domin kuwa su ne suka
bata damar yin nasara a wannan basajar da tayi
min wacce ta kira da wasa, sai dai tayi kuskure da
ta ce ban san yanda a ke buga wasan ba, domin
kuwa ni malamin wannan wasar ne kawai dai
idanuna sun rufe saboda kwadayi da kuma wauta,
shi yasa na kasa gano bakin zareb wasar,
ga shi garin kwadayin nawa na rasa hannuwan da
nake rubutun da su, kuma nake dinki ina neman
abin sakawa a bakin salati. Karyata ta kare....
Shi yasa da na samu sauki naga ya kamata in zo
wa duniyar facebook da wannan labari ko 'yan
uwana samari zasu tsira daga tarkon Basajar
matan social network.
KARSHE WANNAN SHINE KARSHEN LABARIN