Wasu mutane 16 yan dangi daya sun rasu bayan da aka samu wani hadarin mota. Sannan kuma akwai mutane 11 wadanda suka ji raunata.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa hadarin mota ya aiko ne akan hanyar Gwarzo a jihar Kano. Wadanda abun ya aiki gare su a bayyana cewaiIyalin Halilu Getso ne, tsohon ma’aikatacin gidan radiyo ta kasa.
Wani mai bada shaida yace: “Motocin guda 2 sunyi kokarin wuce mota ce sai sukayi karo da babbar mota. Direban motar da sauran mutane 16 take suka rasu.”
Malam Aminu Usman, Kwamanda masu kula da lafiyar manyan hanyoyin (FRSC) ya tabbatar da aukuwar hadarin mota kuma ya bayyana cewa an rufe wadanda suka rasu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.