Gwamnatin jihar Filato da ke Najeriya ta kai karar tsohon
gwamnan jihar Jonah Jang gaban hukumar da ke yaki da
masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC
saboda batan kimanin N200bn a lokacin gwamnatinsa.
Gwamnan jihar Solomom Lalong na zargin tsohon
gwamnan da mukarrabansa da yin sama-da-fadi da
kudaden domin, cewar sa, bai ga ayyukan da aka yi da su
ba.
Gwamnan ya bukaci hukumar ta EFCC da ta kwato
dukiyar da ake zargin sun wawure, ta kuma ladabtar da
su.
Daukar wannan mataki, a cewarsa, ya biyo bayan karewar
wa'adin mako biyu da gwamnatin ta bai wa tsohon
gwamnan da mukarrabansa na su dawo da kudin cikin
girma da arziki amma hakan ya faskara.
A hirar su BBC, Mista Pam Ayuba, kakakin tsohuwar
gwamnatin Jihar Filaton ya musanta zargin.
Ya ce a shirye suke su amsa kirar hukumar ta EFCC
domin gwamnatinsu ta yi amfani da kudin ta hanyar da ta
dace.