Bayan malaman manyan makarantu mallakar
gwamnatin jihar Osun sun kwashe watanni goma
suna yajin aiki gwamnatin ta kaisu kara gaban
kotun ma'aikata dake Ibadan jihar Oyo
Manyan malaman da
gwamnatin Osun ta kai kara sun hada da malaman
makarantar kimiya da fasaha dake garin Ire da
kwalajojin ilimi dake Ilesha da Ilaro da kuma
makarantar kere-kere dake Esa Oke
Lauya Wale Afolabi shi ya wakilci gwamnatin
jihar a kotun. Yace a karkashin doka kafin
ma'aikata su ce suna da kungiya dole ne su yi
rajista da ma'aikatar ayyuka ta tarayya. Wadanda
suke kiran kansu kungiyar malaman manyan
makarantu na jihar Osun basu yi rajista ba kamar
yadda doka ta tanada. Sabili da haka basu da
izinin kiran kansu kungiya har ma su yi yajin aiki.
Lauya Afolabi yace tuni suka rubutawa ma'aikatar
aiki ta tarayya domin su sami tabbacin cewa
kungiyar manyan malaman ta halal ce bata
sabawa doka ba.
Da suke mayarda martani game da karar
malaman ta bakin kakakinsu Dr Shola Ojeniyi
bayan sun kammala taronsu a garin Ire sun ce
lamarin abun takaici ne domin sun dade suna
tattaunawa da gwamnati amma kwaram sai ta
kaisu kara.
Dr Ojeniyi yace gwamnatin jihar Osun da ta dade
tana muamala da kungiyarsu yanzu ta ce bata bisa
doka. Sun dade suna yin yarjejeniya amma haka
kawai gwamnatin ta ce bata yi dasu kuma.
Za'a fara shari'ar mako mai zuwa kuma malaman
sun ce suna shirye.