Israila ta dauki matakan dakile hare haren da
Falasdinawa ke kaiwa kan yahudawa da suka hada
da killace yankunan Larabawa a birinin Kudus.
A Gabas ta Tsakiya, Isra'ila ta
baiwa rundunar 'Yansandan kasar izinin killace
abunda ta kira "cibiyoyin da suke janyo rikici da
zuga a birnin Kudus". Galibin hare haren da aka
kai a yankin sun auku ne a yankunan da Larabawa
suke a birnin na Kudus.
A cikin sanarwar da ofishin Firayim Ministan
Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayar da safiyar
Laraban nan, yace za'a soke takardun izinin zama
na din din din na mutane da suka kasance 'yan
ta'adda, kazalika wadanda suka kai hare hare za'a
a kwace muhallansu.
Birnin na Kudus ya fuskanci wuni mafi muni a ci
gaba da hare hare jiya Talata da Falasdinawa suke
kaiwa. A cikin wannan wata an kashe akalla
yahudawa uku.
Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry
yace zaiyi balaguro zuwa Isrs'ila da yankin
Falasdinu, da zummar tarfa ruwa kan rikicin.
Sakataren yayi magana ne a maraicen Talata
agogon Washington a sashen koyarda dabarun
mulki na jami'ar Harvard.
Title :
Gwamnatin Israila Zata Killace
Yankunan Larabawa dake Birnin
Kudus
Description : Israila ta dauki matakan dakile hare haren da Falasdinawa ke kaiwa kan yahudawa da suka hada da killace yankunan Larabawa a birinin Kudus....
Rating :
5