Bayan sun kwashi dan lokaci suna kai ruwa rana
da kalamun dake tada jijiyar wuya tsakanin
ma'aikata da jami'an gwamnati yanzu gwamnatin
Adamawa ta amince ta biya ma'aikata daga
tallafin da ta samu daga gwamnatin tarayya
Gwamnatin ta amince ta biya albashi da kudaden
hutu da wasu alawus alawus.
Da yake bayyana matsayin da gwamnatinsa ta
cimma gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindo
ya musanta zargin cewa gwamnatinsa na neman
sauya akalan kudaden.
Ya godewa shugaban kasa Muhammad Buhari da
ya fito da shirin tallafin domin jihohi su samu su
biya albashi. Yace kodayake rance aka basu zasu
biya amma ya taimaka kwarai. Abun da
gwamnatin tarayya ta yi zai taimakawa ma'aikata
da talakawa.
Tun farko dai jama'ar na ganin gwamnan nasu bai
shirya karbar ragamar jan mulkin jihar ba. Irin
wadanda ke fadan hakan gwamnan ya yi masu
shagube.
Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Dauda
Maina ya godewa gwamnan da ya kuduri biyan
bashin da wasu suka bar masa ta handame
kudaden da yakamata su biyasu.