Gwamnan jihar Imo Rochas Okororcha ya kai
ziyara Majalisar Dokokin Jihar Kano saboda
neman hadin kan duk 'yan APC su tashi su
taimaka wurin yaki da kungiyar Boko Haram da
ta'adanci a kasar.
Yayin ziyara da ya kai
majalisar dokokin Kano gwamnan ya tattauna da
'yan majalisar akan mahimmancin 'yan
jam'iyyarsu ta APC su samu hadin kai domin
kawar da kungiyar Boko Haram da duk wani aikin
ta'adanci.
Yaki da 'yan Boko Haram ko ta'adanci ba na
shugaban kasa ba ne kawai. Kamata ya yi su hada
kai domin a samu a kawar da matsalar.
Furucin na gwamna Imo ya sa masana harkokin
tsaro da shari'a suka yi tsokaci akan kwamitin nan
na gwamnonin arewa da suka dorawa alhakin
zakulo masu tallafawa 'yan kungiyar ta Boko
Haram da wasu dake aiwatar da ta'adanci
musamman a arewa maso gabashin Najeriya.
Keften Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya yace a
ganinsa harkar tsaro shi ne a sallamawa jami'an
tsaro shi zai kawo mafita. Babu yadda gwamnoni
zasu iya zakulo masu tallafawa 'yan ta'ada sai sun
hada da jami'an tsaro. Jami'an tsaro sun san
yawancin abubuwa. Sun san 'yan siyasa. Sun san
'yan ta'ada. Idan an basu dama zasu zakulosu ba
sai gwamnoni sun wahalar da kansu ko bata
dukiyar jama'a ba.
Shi kuwa Barister Audu Bulama Bukarti cewa ya
yi idan an yi la'akari da dokokin Najeriya
ta'adanci al'amari ne da ya shafi kasa baki daya.
To duk abun da za'a yi ya zama karkashin
shugaban kasa da kuma gwamnatin tarayya. Batun
zakulo wadanda suke tallafawa ta'adanci dokar
2013 ta yi bayani dalla dalla inji Barrister Bukarti.
Ita ma hukumar EFCC akwai ikon da dokar ta bata
dangane da kudaden ta'adanci. Barrister Bukarti
yace saboda haka idin gwamnoni nada wata
shawara da zata taimaka kamata ya yi su
rubutawa shugaban kasa wasika su yi bayani
Title :
Gwamnan Imo Ya Ziyarci Majalisar
Dokokin Kano Akan Yaki da Ta'adanci
Description : Gwamnan jihar Imo Rochas Okororcha ya kai ziyara Majalisar Dokokin Jihar Kano saboda neman hadin kan duk 'yan APC su tashi su taimaka...
Rating :
5