Fadar White House ta shugaban Amurka tace da
alamu gwajin makami mai linzami da Iran ta
gudanar a karshen mako ya sabawa dokokin
Majalisar Dinkin Duniya.
Kakakin fadar white Josh
Earnest yace akwai "shaida mai karfi" da ta nuna
cewa, hukumomin Farisa dake Tehran sun sabawa
ka'idojin d a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin
Duniya ya shimfida dangane da makamai masu
linzami.
Duk da haka kakakin na Fadar white yace wannan
keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya, daban yake
da yarjejeniyar da zata shiga tarihi da manyan
kasashen duniya suka kulla da Iran.
A ranar Lahadi ne Iran tayi bayanin cewa ta sami
nasarar gwajin makami mai linzami da ta kera da
kanta mai cin dogon zango , wanda tace
linzaminsa zai kaishi har inda aka auna shi.
Ahalinda ake ciki kuma, majalisar dokokin Iran ta
amince da kudurin da ya amince da yarjejenkiyar
da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya
shida kan shirin Nukiliyarta.
Kamfanin dullancin labarai na kasar IRNA yace,
wakilan Majalisar Dinkin Duniya su 161 suka ce
sun amince da dokaryayinda wakilai 59 suka ki.
Wasu 13 suka kauracewa shirin baki daya.
A watan jiya ne majalisar dokokin Amurka ta
kammala nazarin yarjejeniyar inda 'yan Democrat
suka hana yunkurin da 'yan Republican suka so yi
na kada kuri'ar nuna rashin amincewa da
yarjejenyar.