Hukumomi a kasar Mexico sun ce kadan ya rage su
damke madugun masu safarar kwaya a kasar,El Chapo
Guzman wanda ya tsere daga gidan yari a watan Yulin
shekarar 2015.
Sai dai kuma Jami'an tsaron kasar ta Mexico ba su yi
karin bayani ba dangane lokaci da kuma wurin da aka yi
kokarin kama madugun ba.
Amma sun ce Guzman din ya ji rauni a kafa da fuskarsa a
kokarin guje wa ma'aikatan.
Shi dai Guzman ya tsere daga gidan yari ne ta wata
hanyar kasa mai tsawon kilomita daya da rabi.
Ya kuma kasance madugun kungiyar safarar miyagun
kwayoyi wadda tayi kaurin suna wajen safarar kwayoyin
zuwa Amurka.
Title :
Guzman ya sake layar zana a Mexico
Description : Hukumomi a kasar Mexico sun ce kadan ya rage su damke madugun masu safarar kwaya a kasar,El Chapo Guzman wanda ya tsere daga gidan yari a ...
Rating :
5