An samu wata girgizar kasa mai karfin gaske a arewa maso gabashin Afghanistan har sai da aka ji karar ta a Pakistan da India, lamarin ya da ya sa mutane suka dimauta.
Rahotannin farko sun nuna cewa a kalla mutane 13 ne suka mutu a kasar Pakistan.
Gine-gine sun girgiza a dukkanin kasashen uku.
Mazauna birnin Kabul sun ce ba su taba jin karar girgizar kasa irin wannan ba.
Kamfanonin sadarwa a kasar Afghanistan sun daina aiki, sannan asibitoci suna cikin shirin ko-ta-kwana.
Hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar, wacce ke da karfin maki 7.5 a ma'aunin ricta, ta fi karfi a birnin Faizabad na Afghanistan da ke cike da tsaunuka.
bbchausa
Title :
Girgizar kasa a Afghanistan
Description : An samu wata girgizar kasa mai karfin gaske a arewa maso gabashin Afghanistan har sai da aka ji karar ta a Pakistan da India, lamarin ya da ...
Rating :
5