A Najeriya rahotanni na cewa, jama'a na guduwa daga
garin Geidam na jihar Yobe sakamakon fargabar yiwuwar
sake fuskantar harin 'yan Boko Haram.
Wani mazaunin garin ya ce, yawanci mata da yara kanana
ne ke ficewa daga garin kuma harkoki sun ragu sosai a
garin.
Koda a wannan makon kasuwar garin ba ta ci ba saboda
fargabar tsaro.
Hakan na faruwa ne sama da mako guda bayan 'yan
Boko Haram sun kai hari garin na Geidam ranar da
kasuwa ke ci inda rahotanni suka ce sun yi awon gaba da
kayan abinci mai dumbin yawa.
Tuni dai rundunar sojan Najeriya ta karfafa samar da
tsaro a garin na Geidam inda aka samar da karin dakaru
da kuma kayan aiki, da kuma bada tabbacin tabbatar da
tsaro.