Gwamnan jihar Borno ya gamu da masu zanga
zanga a garin Jakana dake da tazarar kilomita 40
daga Maiduguri akan karancin ruwan sha da garin
ke fama dashi na kusan shekaru 10.
Mazauna garin Jakana dake
karamar hukumar Konduga a jihar Borno sun
kokawa gwamnan akan matsalar ruwan sha da
suke fama dashi shekara da shekaru.
Gwamnan ya ziyarci garin ne saboda duba wasu
ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa. Yayinda ya
isa garin daruruwan mutane da suka hada da
maza da mata da yara suka fito suna kokawa akan
rashin ruwan sha.
Jama'ar garin sun ce suna sayen ruwa galan daya
daga nera hamsin zuwa dari.
Amma nan take gwamna Kashim Shettima ya yiwa
mutanen alkawarin magance masu matsalar inda
ya bada umurnin tona masu sabuwar rijiyar
bututu. Nan take kuma aka kawo injinan tona
rijiyar.
Gwamnan ya cigaba dacewa banda ruwan sha
zasu cigaba da gina makarantu da samar masu
ababen rayuwa na yau da kullum.
Title :
Garin Jakana dake Borno Na Fama da
Karancin Ruwan Sha
Description : Gwamnan jihar Borno ya gamu da masu zanga zanga a garin Jakana dake da tazarar kilomita 40 daga Maiduguri akan karancin ruwan sha da garin...
Rating :
5