Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ta ci tarar kocin
Chelsea, Jose Mourinho, £50,000, sannan ta haramta
halartar wasa guda, saboda wadansu kalamai da ya furta
game da jami'an wasa.
Mourinho dai ya yi ikirari ne cewa tsoro ne ya hana
jami'an bai wa 'yan wasanshi bugun fanareti bayan da
alkalin wasa Robert Madley ya ya hana Chelsea bugun
tazara a wasan da suka buga da Southampton wanda
suka sha kashi da ci 3-1.
A cewar hukumar ta FA, kalaman Mourinho na nuni da
cewa alkalan wasan sun yi son-kai.
Sai dai kuma za a aiwatar da haramcin da aka yi wa
Mourinho ne kawai idan ya sake aikata laifin a cikin
shekara guda mai zuwa.
Wasan, wanda Southampton ta bi Chelsea har gida ta fi
ta rawa, shi ne na hudu da kungiyar ta Chelsea ta sha
kashi a wasannin takwas din ta buga a farkon kakar
wasanni ta bana.