Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC
ta damke Mr Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar
Akwa Ibom kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar
dattawan kasar.
Bayanai sun ce da yammacin ranar Juma'a ne jami'an
EFCC din suka damke tsohon gwamnan.
Ana zarginsa ne da wawure dukiyar al'umma a zamanin
mulkinsa a jihar ta Akwa Ibom.
Wata majiya a hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ana yi
wa Mr Akpabio tambayoyi a ofishin hukumar da ke
Abuja.
Mr Godswill Akpabio shi ne gwamnan jihar Akwa Ibom
daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A yanzu haka dai EFCC na binciken wasu daga cikin
tsofaffin gwamnoni a Nigeria ciki har da Alhaji Sule
Lamido na Jigawa da Murtala Nyako na Adamawa da
Gabriel Suswan na Benue da kuma Ikedi Ohakim na jihar
Imo.
Title :
EFCC ta damke Godswill Akpabio
Description : Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta damke Mr Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban marasa rin...
Rating :
5