Dan wasan Manchester United, Memphis Depay, da kuma
Robin van Persie na Fenerbahce sun yi cacar baki a
wurin atisayen tawagar kwallon kafar Netherlands.
Kociyan Holland Danny Blind ya tabbatar da aukuwar
lamarin da ya faru kafin buga wasan da suka doke
Kazakhstan 2-1 a ranar Asabar, amma ya karyata cewar
abin ya yi tsanani.
Kocin ya kuma ce kin saka van Persie a cikin 'yan wasa
11 da suka fara wasa da Kazakhstan bai shafi sa-in-sar
da ya yi da Depay ba.
Van Persie shi ne dan wasan Holland da ya fi ci wa
tawagar kwallaye, a inda ya ci 49 daga wasanni 100 da ya
buga mata, kuma na darinne wanda ya yi a ranar Asabar
a inda ya canji wani dan wasan.