Bayan da masu takararar neman Jam'iyyar
Republican ta tsaida su takarar shugabancin
Amurka da suka kara har sau biyu,takwarorinsu a
bangaren Jam'iyyar Democrat sunyi tasu
muhawara ta farko saboda zaben shugaban kasa
da za'a yi badi. Sun gwabza ne a birnin Las Vegas
a daren jiya Talata.
A zamanta ta wacce take kan
gaba a kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a tsakanin
magoya bayan jam'iyyar Democrat, tsohuwar
sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary
Clinton a zahiri da badini ita ce a tsakiya, domin a
yadda aka jera su, ita ce a tsakiyar sauran 'yan
takarar hudu.
A kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a na bayan
bayan nan sakamko ya nuna Hillary ce take kan
gaba da maki 40 cikin dari, sannan babban wanda
yake kalubali takararta Sanata Bernie Sanders
shine yake biye d a ita da maki 25.
Ita dai Madam Clinton wacce take kan gaba aka
jefawa tambaya mafi wuya, cewa tana yawan
canza ra'ayinta domin a zabeta. An bada misali da
yarjejeniyar cinikayya ta baya bayan nan da ake
kira TPP, da kasashe 12 dake yankin Pacific suka
sanya hanu akai.
Madam Clinton ta yarda cewa lokacinda take
sakatariyar harkokin wajen Amurka ta goyi bayan
shirin, ta kara da cewa yanzu bayan shekaru ana
shawarwari kan yarjejeniyar, daidaiton bata cika
mizani na auna shirin ba.
Da aka tambayesu su duka 'yan takarar biyar abu
mafi muhimmanci da ya fuskanci Amurka, 'yan
takarar kowa ya bada amsa daban da na dan
uwansa.Dan takara Lincoln Chafee wanda tsohon
gwamnan jihar Rhode Island ne ya amabci rikicin
da ake yi a gabas ta tsakiya. Martin Omalley,
tsohon gwamnan jihar Maryland ya zabi matsalar
rikicin Nukiyar Iran, Sakatariya Clinton ta zabi
barazanar Nukiliya a duniya baki daya, Senata
Bernie Sanders ya dauki batun canjin yanayi.Shi
kuma tsohon Senata Jim Webb ya nuna
danganatakar Amurka daChina da kuma
barazanar tsaro a internet da kasar Sin din take
yiwa Amurka.
Ba kamar takwarorinsu na Jamiyyar Republican
ba, su 'yan takarar na jam'iyyar Democrat basu
bata lokaci suna sukar juna ba, sunyi amfani da
zarafin na jiya Talata wajen bayyana manufofinsu
da irin ayyuka da suka yi a baya.
Title :
'Yan Democrats dake Neman
Shugabancin Amurka Sun Yi
Muhawarar Farko
Description : Bayan da masu takararar neman Jam'iyyar Republican ta tsaida su takarar shugabancin Amurka da suka kara har sau biyu,takwarorinsu a b...
Rating :
5