Za a yi wa wani dan Biritaniya mazaunin Saudiyya bulala
sama da 360 saboda ya mallaki giyar da ya hada da kan
shi a gidan sa.
Tuni dai Karl Andree mai shekaru 74, ya shafe shakera
daya a gidan yari bayan an kama shi da kwalaben giya
guda shida a but din motarsa.
Iyalan Mr Andree sun ce hukumomin Saudiyya sun sa su
sun yi zaton cewar ba za a yi masa bulalar ba saboda
shekarunsa da kuma rashin lafiyar da yake fama da ita.
Amma kuma suna fargabar za a iya sake shawara.
Gwamnatin Biritaniya ta nemi a sake shi ba tare da bata
lokaci ba.