Masana Najeriya na kira ga gwamnati da al’umar
kasar da su koma harkar noma domin a ciyar da
kasar gaba ganin cewa da kudaden noma aka gina
Najeriya ta kai matsayinta na farko a idon duniya.
A cewar tsohon shugaban
hukumar hadahadar kasuwanci ta Chambers of
Commerce, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, an gina
Najeriya ne da albarkatun noma.
“Najeriya da ta dogara ne da noma da sana’oin
hannu, da kudin fata da na kirgi da na gyada da
na auduga da na ridi da na cocoa hatta kudin da
aka hako mai da kudin wadannan noma aka yi
amfani.” In ji Dayyabu a wata hira da ya yi da
Sasshen Hausa na Muryar Amurka.
A cewarsa yanzu ya rage ne ‘yan Najeriya su
koma ga Allah su zabo shugabanni na gari domin
a fitar da kitse daga wuta.
“Kuma Allah da ikonsa sai ya kawo wanda ya ke
da zafin da kimar da kuma kokarin ya ga ya yi
wadannan abubuwan, amma kuma shi ba dan
siyasa ba ne kuma ya kasa tunanin yadda zai
janyo ‘yan siyasa a jikinsa ta yadda za su rinka
tunatar da shi kan abubuwa.” Ya kara da cewa.
Title :
Da Noma Aka Gina Najeriya- Masani
Description : Masana Najeriya na kira ga gwamnati da al’umar kasar da su koma harkar noma domin a ciyar da kasar gaba ganin cewa da kudaden noma aka gin...
Rating :
5