Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC
ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Usman
Dakingari domin ya masa tambayoyi a kan zargin wawure
dukiyar al'umma.
Kakakin EFCC, Mr Wilson Uwujaren ya tabbatar wa BBC
cewar da safiyar ranar Litinin aka gayyaci Dakingari inda
ya je ofishin na EFCC a Abuja domin ya amsa tambayoyi.
Dakingari wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin
gwamnan jihar Kebbi daga shekarar 2007 zuwa 2015 a
karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma ya na daga cikin
manyan 'yan siyasa da ake zargin da cin hanci a Nigeria.
Ko a ranar Juma'a ma sai da EFCC din ta damke, tsohon
gwamnan jihar Akwa Ibom Mr Godswill Akpabio wanda a
yanzu shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar
dattawan kasar, shi ma a kan zargin cin hanci da karbar
rashawa.
A yanzu haka dai EFCC na binciken wasu daga cikin
tsofaffin gwamnoni a Nigeria ciki har da Alhaji Sule
Lamido na Jigawa da Murtala Nyako na Adamawa da
Gabriel Suswan na Benue da kuma Ikedi Ohakim na jihar
Imo.
Title :
Cin Hanci: EFCC ta gayyaci Dakingari
Description : Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Usman Dakingari domin ya masa tambayoyi ...
Rating :
5