Wani kamfanin bincike ya ce a karon farko, hamshakan
attajiran da su ka kai matsayin biloniya a China sun
wuce na Amurka.
Rahoton na kamfanin Hurun, da ke Shanghai ya ce a
yanzu China tana da attajiran suka kai matsayin biloniya
su 596 a yayin da Amurka ke da biloniya 537.
Yawan attajiran China na ci gaba da karuwa duk da koma
baya da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.
Rahoton Hurun ya ce akwai wuya wajen tattara alkaluman
masu hannun da shuni kuma watakila adadin a zahiri ya
nunka abin da aka wallafa.