Hukumar kwallon kafar Afrika, CAF ta fitar da jerin
sunayen 'yan wasa 37 wadanda za su yi takarar "gwarzon
dan kwallon Afirka" na shekarar 2015.
Yaya Toure, dan wasan tsakiya na Ivory Coast da
Manchester city, wanda shi ne ya lashe gasar a shekarar
da ta gabata, ya shiga jerin 'yan wasan da hukumar ta
fitar.
Kazalika, an fitar da sunayen Gervinho da Max Gradel da
kuma Serge Aurier a matsayin wadanda za su yi takara.
Wasu a cikin jerin sunayen sun hada da Andrew Ayew
dan Ghana na Kulob din Swansea City da Ahmed musa
dan Najeriya na kulob din CSKA Moscow; Sadio Mane
dan Senegal na kulob din Southampton da Pierre-Emerick
Aubameyang dan kasar Gabon, na kulob din Borussia
Dortmund da Vincent Enyema dan Najeriya na kulob din
Lille da kuma Riyad Mahrez dan kasar Algeria na kulob
din Leicester city.
Za a ci gaba da tace sunayen mutane 37 din zuwa 10 a
watan Nuwamba kafin a kuma ragewa zuwa sunaye
biyar, sai kuma a rage zuwa ukun karshe kafin a yi bikin
bayyana wanda ya lashe gasar.