Wata kotun soji a Nigeria ta sanar da korar wani Janar
din soja bisa zarginsa da sakaci a yaki da kungiyar Boko
Haram.
Kotun sojin ta sanar da sallamar Brigadiya Janar Enitan
Ransome Kuti daga aikin ne bisa sakacinsa har 'yan
kungiyar Boko Haram suka kwace garin Baga tare da
kwashe dimbin makamai na sojin kasar.
A watan Mayun da ya gabata ne aka gurfanar da Janar
Ransome Kuti a gaban kotun sojin da ke zamanta a
barikin Mogadishu da ke Abuja tare da sauran sojojin da
ake zargi da sakaci a yaki da Boko Haram.
A watan Junairun bana ne dai 'yan Boko Haram suka kai
hari a Baga inda suka kwace iko da garin, kafin dakarun
Nigeria su kwato garin bayan wasu watanni.
A shekara ta 2013, an kona gidaje kusan 2,000
sakamakon wasu hare-hare a garin Baga mai kan iyaka
da jamhuriyar Chadi.