Jami'an tsaro a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar
soji biyu sannan ukku kuma sun sami raunuka a wani
harin kunar bakin wake a Diffa.
Ministan tsaron kasar, Mahamadou Karidjo, ne ya
tabbatar da hakan inda ya ce sojojin sun rasa rayukansu
ne yayin da 'yan Boko Haram suka tayar da bama-bamai.
An kai harin ne a kusa da wani gari da ke yankin Diffa.
Wasu mazauna garin na Diffa dai sun ce an shafe daren
ranar Talata ana jin karar harbe-harbe tsakanin jami'an
tsaro da 'yan kungiyar ta Boko Haram.
A yanzu haka dai yankin Diffa ma karkashin dokar ta-baci
a wani mataki na hukumomi domin su kawar da 'yan
Boko Haram.
'Yan gudun hijira kimanin 150,000 daga Najeriya ne ke
zaune a yankin domin tserewa hare-haren da Boko
Haram ke kai musu.
Title :
Boko Haram: An hallaka sojoji biyu a Diffa
Description : Jami'an tsaro a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar soji biyu sannan ukku kuma sun sami raunuka a wani harin kunar bakin wake a D...
Rating :
5