Kasar Ghana tana shirin kulla wata yarjejeniya da
Najeriya ta sayen iskar gas a kan kusan $103m bayan
kamfanin gas da ke Najeriyar ya janye aniyarsa ta hana
bai wa Ghana isakar gas din.
Ghana ta sha gwagwarmaya wurin biyan kudin iskar gas
din da take saye daga Najeriya tun bayan da kamfanin
samar da wutar kasar Volta River Authority (VRA) ya
shiga halin rashin kudi sakamakon daina aron kudi
bankin da ta yi saboda kudin ruwan da ake tsawwalawa.
Kamfanin VRA ya daina biyan Najeriya kudin iskar gas
tun watan Agustan bara, amma gwamnatin Ghana ta biya
$10m a makon jiya, hakan kuma ya bude hanya domin
tattaunawa game da tsarin da za a bi wurin biyan sauran
bashin.
Kamfanonin samar da wutar Ghana na cikin matsala
sakamakon karancin kudi da rashin kayan gudanar da
ayyuka a kogin kasar da kuma satar wutar lantarki da
'yan kasar ke yi.
Ana amfani da iskar gas din aka zuko daga Najeriya, ta
hanyar kasashen Benin da Togo, wurin samar da kashi
daya cikin hudu na wutar lantarkin Ghana, dalilin haka
kuwa katse wutar zai iya janyo wa kasar koma baya.
Matsalar kuma za ta iya shafar siyasar shugaba John
Mahama, wanda ya sha alwashin kawo karshen matsalar
wutar lantarki a Ghana kafin farkon shekarar 2016.