Gwamnatin jihar Neja ta fito fili tace bata da
hannu a batun cire Alhaji Ahmed Ibeto daga
sunayen ministocin da shugaban kasa Muhammad
Buhari ya mikawa majalisar dattawa domin
tantancewa.
Ba zato ba tsammani
shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata
Bukola Saraki ya fitar da wata sanarwa daga
shugaban kasa inda ya bayyana cire sunan Alhaji
Ahmed Ibeto na jihar Neja daga sunayen
ministocin da zasu tantance.
Dr. Ibrahim Doba kakakin gwamnan jihar Neja
yace gwamnatin jihar bata ce a cire sunan kowa
ba.
Kodayake babu wani cikakken bayani daga fadar
shugaban kasa dan majalisar wakilan Najeriya
daga jihar Neja Abubakar Lado Suleja yace yana
ganin maganar mutunta bangare bangare ne ya
kawo hakan.
Wakilin yace manyan shugabannin gwamnatin
jihar, wato gwamnan jihar da sakataren gwamnati
daga bangare daya suka fito da shi Ibeto. Tunda
aka ambaci sunansa mutanen bangaren gabashin
jihar suka fara korafi suna cewa an dannesu.
To amma na hannun daman Alhaji Ibeto Alhaji Isa
Adamu yace sun bar wa Allah komi amma
maganar mutunta bangare bangare ba dalili ba
ne.