Abin da babu gardama a ciki shi ne: Allah cikin ikonsa ya daure tsakanin aure da sha'awar irin ta saduwa, bai bar abin a sake ta yanda sai an yi auren sannan a yi sha'awar mace ko ita ta yi sha'awar namiji ba, wata-qila da mutane -tsakanin maza da mata- an guji wannan Sunnah mai qarfin gaske, sai Allah SW ya sanya saduwar ta zama ginshiqi mai qarfi ga rayuwar dan adam kamar cin abinci, barci da shaqar numfashi, kenan dole mutum ya buqaci saduwa, sai dai kuma in bai bi ta halas ba dole zai bi ta haram.
.
A shari'ance aure ibada ne kuma neman kusanta ne ga Allah SW, domin in da mutum zai sadu da iyalinsa, duk da cewa su biyun buqatunsu suka biya, har wata lada zai samu a wurin Allah SW matuqar dai ya tsarkake aikinsa da kyakkyawar niyya, shi ya sa muke ba da shawarar cewa kar mutum ya fara neman aure kawai don sha'awar yarinyar da ya yi, wanda galibinmu kyawun jiki da fuska da iya ado da magana yake fisgar hankalimmu, mu yi kuma tunanin cewa ibada ne aure har ma saduwar, a wani hadisi na Muslim da na karanta na iske inda Annabi SAW yake cewa:
.
"Akwai sadaqa a saduwar dayanku da iyalinsa" sai (sahabbai) suka ce: Ashe dayammu zai biya buqatar sha'awarsa sannan kuma a ba shi lada a kai? (Annabi SAW) ya ce "A ganinku da a haram ya yi fa (wato fahasha kamar zina da auren holewa), shin akwai zunubi a kansa?" Suka ce: Qwarai kuwa. Ya ce " To haka kuma in ya saka a cikin halas (wato a aure na shari'a) yana da lada. Muslim, Abu Dawoud, Ahmad.
A wani addini ne za ka sami irin wannan gatar? A hana kowa ya ji qamshin matarka, a hana shi ganin kwalliyarta ko wani sassa na jikinta bare ya tabi jikinta koda da musafahar gaisuwa ne sai dai kai kadai kawai?
.
Sannan ka sadu da ita kamar yadda kowace dabba take saduwa da daya jinsin, amma kai taka saduwar ta zama ibadar da Allah SW zai ba ka lada a kai, ko ma na ce ta zama hanya ta neman kusantaka ga Allah SW kamar sauran nau'o'in ayyukan sadaqa? Wannan shi ne muslumci, wanda yake daukaka saduwar namiji da mace abu mai daraja mai girma, ya mayar da abin da ake gani kamar al'ada ne ya koma ibada, wanda ake gani kamar hanyar rage sha'awa ce ta zama hanyar neman yardar Ubangiji.
.
Wato dai babban abin da ake buqata wurinka kai mai neman aure, ko ita mai amincewa a aure ta shi ne: A sami tsarkakakkiyar niyya wace ya za ta kawar wa mutum da tunanin cewa zai nemi aure ne kamar yadda ya taso ya ga ana yi, ta sanya masa a zuciya cewa ya kai matsayin da zai fara wata ibadar qari a kan wace yake yi, bautar Allah kuwa ba a yin ta da saba masa, dole tunanin mutum ya zama kame ido, kunne, hanci da gaba daga saba wa Allah, ba wai kuma a yi aiki da sabon wajen neman aure ba.
.
Dole dai manufar ta zama buqatuwar kamewa ne da nisantar holewa da diyoyin jama'a, da kuma cin ma manufar da Allah SW ya halicci mutum a dalilinsa, wato samun zuriya ta gari, wace in ba ta ba yadda za a yi adadin jama'a ya ci gaba da habaka har duniya ta sami jama'ar da za su zauna a cikinta, don haka da Allah SW ya hana saduwa da mata a ranakun azumi ya ce (To yanzu ku take su, ku nemi abin da Allah ya wajabta muku), wato ba manufar aure ne ba kawai a kawar da sha'awa, har da qaunar juna da hayayyafa yadda Annabi SAW zai yi alfahari da al'ummarsa ranar qiyama.
.
A nan ne za ka ga son kan maza, yadda da zarar ta haska masa a ido ta liqe 'yar muryarta gami da murmushi, ga qamshi da kwalliya, shi kenan ta gama da shi, ba ruwansa kuma da tunanin ko za ta iya riqe masa 'ya'ya ko ba za ta iya ba, bare kuma ya yi tunanin dabi'unta da halayenta, abin da ya sa a gaba kawai shi ne, in dai ta shigo gidansa komai zai canja, don ba zai yarda da diban albarka ba, lamarin kuwa ba haka yake ba, mace in Allah ya mallaka maka ita, matuqar za ka yi mu'amalla da ita kamar yadda muslunci ya tanadar, to tun farko ka nemi ta gari kawai, ba abin da ya fi ruwa taushi amma kisa yake....
Title :
Bambanci Sha'awa Da Soyayya Part 14
Description : Abin da babu gardama a ciki shi ne: Allah cikin ikonsa ya daure tsakanin aure da sha'awar irin ta saduwa, bai bar abin a sake ta yanda ...
Rating :
5