Ita ma batacciyar soyayyar tana da tata tasirin wanda alamunta suna bayyana ya zama dole ga mutum ya nemi magani:-
a) Mutum ya gaza bayar da aikinsa kamar yadda ya dace, don zuciyarsa
kullum tana wajen wata, duk dan abin da ya samu ya bakka ta, in ba ta
karba ba hankalinsa ya tashi, ya gaza tsayuwa a wajen aiki don yana son
ya je wajen masoyi, a irin wannan matsayi dole a nemi matsaya, don ba
ingantacciyar soyayya ake yi ba, sha'awa ita ce a kan gaba, da zarar an
daura aure ita matar za ta fara ganin wasu 'yan canje-canjen da ba ta
taba tsammani ba.
.
b) Akan sami kuma qunci da damuwa, masamman
idan ya kasance mutum ya yi nesa da masoyi, wani lokaci mutum yakan rasa
abin da yake masa dadi, har da kansa ya yanke hukuncin cewa maganin
hakan kawai shi ne kasancewa da masoyi, amma da a ce ingantacciyar
soyayya ce, ba a yin ta inda bai dace ba, don soyayya ce da ba a rabuwa,
kuma ita masoyiyar tana da damar gamsar da shi da duk abin da yake
buqata, kuma a lokacin da yake so, a nan ba za a sami hauhawar sha'awa
ba, sai dai son saduwa da masoyi gami da yi masa hidima.
.
c)
Qoqarin zama da wanda ake kira masoyi ne na gaskiya kowani lokaci, da
son taban jikinsa in zai yuwu, ko taban wuraren fitina duk dai da sunan
soyayya, mutum shi a kan kansa ya san ya sabi Allah, zuciyarsa za ta yi
ta raya masa cewa Allah fa zai yi fushi da shi, wannan in yana da dan
sauran imani kenan a zuciyarsa, na zauna da wani mutum da yake ce min ya
kai matsayin da budurwar ta yi masa tayin biya masa buqata matuqar yana
so, tsoron a kama su ne kawai ya hana shi, amma duk wani nau'i na sabo
ya aikata, a nan zai kira sha'awar da take tsakaninsu ne da sunan
soyayya, wata qila ma su ce soyayya ce ta gaskiya, alhali sam ba haka ba
ne, tasirin batacciyar soyayya ne.
.
d) Akwai kuma nisantar
'yan uwa da abokai, da ma kowa da kowa don dai a kadaitu da wanda ake
ganin masoyi ne, duk in ka raya wa zuciyarka cewa ba wanda zai hana ka
zama da wance, ko kuwa ita ta ce in sama da qasa za su hadu sai ta auri
wane, ba shakka wannan tasirin makauniyar soyayya ne, wanda ake ce ma ta
"hana ganin laifi" irin wannan ko abokkai da qawaye ba su cika ba da
gudummuwar a zo a gani ba wajen taimakon masoyan, domin abin da
masoyiyar take so qawarta take ba ta shawara, shi ma saurayin bai samun
gamsasshiyar shawara wajen abokansa sabo da wannan dalilin.
.
Domin a taimaka wa wadannan masoyan dole a bi wasu 'yan shawarwari:-
a) Ka zabi babban dalilin da ya sa kake son wance, ko dalilin da zai sa
ta karbi soyayyar wane, kar ya zama cewa kyawunta kawai da tsarin
surarta suka pisgi hankalinsa, ko ita ta sakankace cewa zai iya biya ma
ta buqatunta na rayuwa da zumunci don haka za ta aure shi, a yi qoqari a
duba lamuran da ba sa canja wa mutum, kamar dabi'u na qwarai, son
ibada, neman ilimin addini, ko shiryarwa ta qwarai.
.
b) Ya zama
dole a nisanci kallon fima-fiman batsa, da karanta littafansu, a
nisanci zama da wani jinsi na daban, da son ganin wuraren da suke motsa
sha'awa a jikinsa, yanzu har hotuna na batsa da bidiyo ana iya kallo a
wayoyi, su kuma sukan qara sha'awar da in mutum bai yi a hankali ba ba
shakka zai fada zuwa ga batacciyar soyayya wace qarshenta nadama ne, ba
ina wajabta sanya niqabi ne ba wajen hira da masoyi, ko hana zance gaba
daya, amma dole a guji abin da zai dauwamar da sha'awa a maimakon
soyayya.
.
c) Kusantar Qur'ani mai girma, da koyarwar Annabi SAW
a hadisai tana matuqar taimakawa wajen rage aukawa cikin baqar soyayyar
da take qarewa da nadama, masamman zama a wuraren karatun addini, inda
ake gina mutum don ya fahimci aure ibada ne, nemansa kuma yana da tsari
yadda addini ya wasafta, ba abu ne da mutum zai yi yadda ya ga dama ba,
duk lokacin da mutum ya sami kansa ba ya aikin komai to ya daure ya nemi
abin da zai shagalta da shi, masamman 'yan karance-karancen abubuwa
masu amfani.
.
d) Mutum ya yi qoqari ya sanya wa zuciyarsa cewa
soyayya kamar dambe ce; Wanda yake kallo shi yake ganin da zai naushi
wuri kaza tabbas zai yi kaye, kai da kake ciki ba ka da sararin da za ka
iya hango wurin, don haka sauraron shawarwarin abokai da na gaba suna
matuqar taimaka wa matashi wajen gyarar rayuwar soyayyarsa, kar mutum ya
ce ya fi kowa sanin abin da ya dace da shi, raina shawarwarin uwaye
alama ce babba ta makauniyar soyayya.