4) Soyayya ta quruciya ta bambanta da sauran da aka ambata a baya in
ba ta farko ba, soyayya ce da galibi ba ta da dalili sama da burgewa,
'yammata sun san abubuwan da suke burge samari da su na kwalliya da ado,
don haka a shirye suke su yi wa saurayin da suke qauna duk abin da yake
buqata, ko wanda suka tabbatar zai ja hankalinsa, galibin abin da ake
musayarsa a tsakaninsu yana da alaqa ne ta kai tsaye da zuciya zalla,
don haka dole sha'awar saduwa ta zama ita ce qoli-qoli da komai.
.
Soyayyar quriciya ta fi tsanani ne wurin:-
i) Son ganin juna da qaunar zama da juna, a dai sami wani dalili na
mannuwa da juna, ko jin sassanyar murya, da musayar murmushi da dariya
cikin zazzaqar murya mai motsa sha'awar juna, kwalliya da nau'o'in ado
da turare abubuwa ne da ake amfani da su don burge juna, in budurwa za
ta zauna da saurayi ko a dakin mamanta ne sai ta qure adaka, mai yuwa ma
ta sanya takalma masu tsada, don dai ta tabbatar da ta burge shi, a
zatonta in zai qaunace ta sosai ta wannan hanyar, akwai yuwuwar samun
dauwamammiyar soyayyar.
.
Shi kuwa namiji ba shakka yaqi yake yi
na a mutu ko a yi rai, galibin samari, masamman a matattarar da ake
samun kudi a hannun samari, ba abin da suka fahimci soyayya kamar juya
wannan kudin wajen mallakar zuciyar mace, qoqarin saurayi kawai budurwar
ta fahimci cewa zai iya gamsar da ita komai, masamman abubuwan da suka
shafi rayuwa, shi ya sa ko bashin kudi zai yi don ya ba ta, ko ya ma ta
wani abu na burgewa abu ne mai matuqar sauqi, ko da kuwa ba ta nema ba,
har aron kaya ko mota don zuwa zance abu ne mai matuqar sauqi, na zauna a
wata matattara wace sai budurwa ta ga irin ginin gidan saurayin kafin
ta yarda a fara soyayyar.
.
ii) Rashin binciken yuwuwar rayuwa
cikin fahimtar juna, da wahala saurayi ya tsaya duba yuwuwar cikakkiyar
musayar motsin rai da mace kafin ya fara nemanta, wasu za ka taras
karatu ya hada su, sai sun gama shaquwa da juna kafin a fara zancen zuwa
gidajen juna, sau da yawa shawara kan rabuwa ko wani bincike yakan zama
sharhin bayan labarai ne kawai, amma bai da wani tasiri ko kadan, duk
wani hange da iyaye suke yi bai da wani amfani don ba sa daukar duk wata
shawara da ta saba wa mannuwarsu da juna, koda mummunan halin masoyi ya
bayyana sukan raya cewa za su iya canja shi a lokacin da suka zauna da
juna, ba tare da nazarin cewa wata dabi'ar ba ta sauyuwa cikin sauqi ba.
.
ii) Yadda za ka tabbatar da cewa soyayyar ana yin ta ne kawai ido rufe
ba tare da lissafi ba, da zarar masoyi ya sami tasgaro sai ka ga ya
ruguje gaba daya, yana iya gaya maka kai tsaye cewa ya yi asarar da ba
zai iya maido da ita ba, duk da cewa babu wata hidima ta jiki da aka yi
cikin sakewa da natsuwa a tsakanin juna, ba saduwa ta auratayya a
tsakaninsu ta ina soyayya ta kammala bare mutum ya san ya yi asarar
rabin jikinsa? Soyayya ta gaskiya ba ta hana tunani da sanya komai a
mahallinsa, ita jagoranci ma take yi don kai masoyi zuwa ga biyan
buqatarsa amma ta hanyar da ta dace.
.
iv) Soyayyar quruciya
gaba dayanta saqe-saqen zuciya ne ba tare da tabbatarwa ta hanyar da ta
dace ba, wasu abubuwan zai yi wahala matattara su karba to bare kuma
addini, Annabi SAW ya nusar kan haka don a sami wani shinge a tsakanin
wadannan masoyan don tsoron aukawa kwazazzabon da-na-sani, iyaye kuma a
yau suna taimakawa sosai wajen ba wa 'ya'yansu damar su kutsa cikin
tekun sha'awar juna kafin saquwar soyayya ta gaskiya.
.
v)
Ginuwar makwancin soyayya a zuciya kadai ba tare da tanadin qwaqwalwa da
sauran sassan jiki ba abu ne sananne a soyayyar quruciya, in da za ka
tsare saurayi ko budurwa ka yi wa dayansu tambayar qwaqwaf kan cewa: Don
me kake son dan uwanka? Bai iya cewa ga dalili sama da buqatarsa ta
kansa shi kadai, da wahala ya yi tunanin alaqar matar da iyayensa, ko
'ya'yansa bare kuma 'yan uwansa, wani abu ya gani a jikinta ya burge
shi, ko ita ta gani a tare da shi ya ba ta sha'awa, amma tana da damar
tambayar kanta: "Shin wanga ya dace ya zanto uban yarana?"
.
vi)
Kasancewar soyayyar quruciyya a zuciya kadai take, juyawarta abu ce mai
matuqar sauqi, don ita kanta zuciyar ba ta da gaba guda, a don haka ko
magana ce aka ce ta zuci ce ba a daukar ta da wani mahimmanci, don an
san yadda take, duk yadda soyayyar quruciya ta kai da habaka, in dai ba a
gina ta a turba qaqqarfa ba to ka san cewa shekaru na qaruwa ne
qarfinta yana raguwa, don qyalqyalin abin da ya sa aka gina ta shi kansa
ya fara dushewa.
Barkanku da fara shiga dare..!