Soyayya ta gaskiya tana nufin saduwa ne da juna a jiki da zuciya, ta
yadda masoyi zai yi ta fatar a jingina shi da masoyinsa, in a ka ce wane
masoyinka ne, dadi za ka ji ko da ma tsokanarka aka yi, sam ba za ka ji
zafi ba bare kuma ka hasala, don an kai matsayin da kake jin masoyinka
tamkar rabin jikinka, ba ka qaunar baqin cikinsa kamar yadda ba ka fatar
damuwarsa, lokacinka, kudinka, hidimarka, jikinka da duk wani abu da ka
mallaka na ka ne matuqar bai buqata ba, ba ka damu ka sha madaci ba
matuqar shi zai ji zaqin zuma, kuma za ka iya yin kuka don dai ka ga
dariyarsa.
.
Masoyi shiri ake yi masa na taimako ta kowace sifa,
ta yadda za ka gyara komai na ka dominsa, sannan ka yi tattalinsa da
'ya'yansa da duk wanda ya jibance shi, ka qarfafa zumuntarsa, ka kare
mutuncinsa da sunansa, ka tsaya tsakaninsa da duk abin da zai iya jefa
shi cikin damuwa ko tashin hankali, ka kwadaitar da shi a kan duk wani
abu da addini ya kwadaitar, ko ya wajabta a yi, ba shakka wannan abu ne
mai tsada, wanda yake buqatar kula da shiri na tsawon lokaci, ba yadda
za a yi daga kallo daya a sami lamunin komai, sannan yawan zama da
namiji ko mace don hira, ko adon mace da abin hannun namiji ba su suke
ba da wannan amincin ba, binciken dabi'ar mutum da tarbiyya ta qwarai su
suke tabbatar da dauwamammiyar soyayya.
.
In don mu kasa
nau'o'in soyayya da qauna ne, haqiqa za mu iya kasawa har gida Bakwai,
wasu sukan taru wa mutum guda, sai ka ga ya iya musayar soyayya kamar
yadda ake buqata, duk yadda aka rasa wani sai ka ga soyayyar ta ragu,
kenan kowa bai rasa qauna da soyayya a tare da shi, sai dai kuma da
fuskar da yake fassarawa ne, in abokin soyayyar ya ga bai samun damar
yin musaya ta daya daga cikin bangarorinta sai ka ga ya damu, shi ma sai
ya sami rauni ta wasu bangarorin.
.
Daga cikin rabe-raben soyayya akwai:-
1) Qauna ta sha'awa: Wannan tana iya samuwa ne daga kallon fari, tsarin
halitta, ko kyawun ado da iya wanka, ko shaharar namiji da abin
hannunsa, ko ma iya zance da lallaba, galibin irin wannan qaunar ana
ganinta a fima-fimai da sauran littafan soyayya, takan yi qarfin da ba a
taba zato ba, ta burge kowa da kowa, masamman ta fuskar yadda ake
gudanar da ita, sai dai da zarar an kawar da sha'awar shi kenan ta tafi,
sai kuma zaman haquri, irin wannan soyayyar ita ce iyayemmu suke
tsokaci a kai da cewa: Da zarar an yi aure ta qare sai kuma zaman
haquri.
.
2) Wata soyayyar tabbas akwaita amma tana da alaqa ne
da haihuwa da qaunar zama uwa ko uba, wato dai buqatar namiji a ce masa
baba, ko mace a ce ma ta mama, masamman in tsararraki sun sami gidajensu
na kansu, an fara lissafin cewa wane 'ya'yansa kaza, ko wance 'ya'yanta
kaza, in irin wannan soyayya ta maqure mutum takan yi masa illa, domin
tana da qarfin da za ta sanya shi ya dauki kowani irin mutum, koda bai
dace a rayu da shi ba, ita kam ana iya jure ma ta, amma ba dole ba ne a
sami musayar motsin rai da faranta wa juna.
.
An yi wasu bayin
Allah da suka so junansu amma Allah Bai ba su haihuwa ba, ganin halin da
uwargidan ta fara shiga, sai maigidan ya ba da shawarar cewa su auro
wata wace za ta hayayyafa musu, amma komai za su kasance kamar yadda
suke, Allah ne dai mafi sanin gaskiya, maigidan ya musluntar da wata, ya
kuma aura, har ta haifa masa 'ya'ya biyu, sai mai rabo ya raba su,
uwargidar ta kwashe 'ya'yan da hujjar cewa ba za a kai musu diyoyi inda
babu muslunci ba, a taqaice dai amaryar ta bar gidan na tsawon lokaci ba
ta yi aure ba, kuma tsohon maigidan na ta yake daukar nauyinta.
.
3) Sai kuma soyayya ta gaskiya, wannan ba ta furuwa lokaci guda, wai
daga zarar ka ga mutum shi kenan kuma ya zama masoyi, wai har kana iya
fadawa rijiya a dalilin raba ka da shi, ka zagi kowa ka saba wa iyaye a
dalilinsa, soyayya ta gaskiya cike take da tsarin da matattara ta
shirya, addini kuma ya tanadar, iyaye sukan ba da gagarumar gudummuwa
wajen tabbatar da ita, addini kuma ya yi wa mutum seti ya nuna masa
abubuwan da suka dace da wadan da dole ya rabu da su don samun natsuwa
da dan uwansa masoyi, wannan tarbiyar mutum take sakawa ya gwanance
wajen zama tamkar masoyinsa a lokacin da yake gida ko lokacin da baya
nan.