Zai yi matuqar wahala mutum ya iya tantance haqiqanin ma'anar soyayya,
don takan canja ta dauki surori daban-daban da launuka mabambanta
gwargwadon mutanen da suke yin ta, akwai buqatar kallon zamani: Ba dole
ba ne soyayyar da aka yi ta a shekara 50 ta zama ita ake yi a yau, Wuri:
Irin soyayyar da ake yi a qasar Turai takan bambanta da wace Larabawa
da mu baqaqe muke yi.
.
Shekara: Manyan mutane da matasan da
suke tasowa kowa da yadda yake nuna qaunarsa ga masoyinsa, dattijo ba
zai sauko ya zama yaro qarami ba, ba ruwan soyayya da tsufa, amma akwai
qaruwar hankali da sanin ya-kamata, Wadata da rashi: In mai wadata zai
nuna qaunarsa ga masoyiyarsa yana da hanyoyin da yake bi, masamman wajen
yin amfani da abin da yake hannunsa wajen zaben inda za a je, da inda
za a zauna, da abin da za a ci.
.
Aure: Akwai cikakken 'yanci
wajen yin amfani da duk wasu lafazozi, da yin aiki da duk wata gaba don
nuna soyayya, ga cikakkiyar hidima don jin dadin masoyi, wannan bai
samuwa a samartaka zalla ba tare da aure ba, Ilimi da jahilci: Wanda ya
yi karatu ya hadu da jama'a daban-daban masu sifar rayuwa mabambanta
gami da cakuda da fahimtar Turawa, dole tsarin soyayyarsa da mace ya
bambanta da wanda bai je makaranta ba, to kafin mutum ya tantance
ma'anar soyayya yana da buqatar ya kalli qusurwoyi da dama, gami da
nazari kan bambance-bambancen matattaran jama'a da addinansu.
.
Annabi SAW yana cewa: Dayanku ba zai yi imani ba har sai ya so wa dan
uwansa abin da yake so wa kansa. Haka qauna take, duk wani mai yin
magana a kan soyayya za ka ji ya qare kan musayar qauna ta kowace sifa,
in mace za ta fito da zuciyarta gaba daya ta danqa wa namiji, to lallai
akwai buqatar shi ma ya yanke hannayensa ya miqa ma ta, soyayya a
taqaice hidima ce ta zuciya da sauran gabobi ba tare da sauraron godiya
ko tukwici ba, aiki take sanyawa tuquru na taimakawa, tausayawa,
tausasawa da ba da kariya, kenan ba kamar yadda ake rayawa cewa tana
hana ganin laifi ba, takan yi qoqarin maganin laifin ne kafin ya auku,
in ya bayyana kuma ta yi qoqarin gyarawa ba lullubewa ba.
.
Ba
yadda za a yi soyayya ta zama wata hanya ta biyan buqatar wani shi
kadai, ko ta taqaitu da amfanuwa da abin da yake hannun wani, shi ya sa
ma Annabi SAW ya ce: Ka guji abin hannun mutane sai su ma su so ka. In
qauna ta taqaita da zuciya sai ta koma sha'awa, wace take kamar wutar
kara mai balbala da macewa a dan lokaci kadan, shi ya sa in mutum ya yi
nazari mai zurfi zai fahimci shawarar da Annabi SAW ya bai wa masoya
wajen zaben abokin rayuwa, sai ya lissafo abubuwan da galibi su suke
daukar hankalin mutum wajen zaben abokin rayuwa.
.
In mace tana
da dukiya tabbas za a yi sha'awar aurenta don abin hannunta, haka in
mutum yana da hali bai rasa samun wace zai zauna da ita komai muninsa,
kenan zancen kudi ake yi, ba kuma hanyar da za a fassara kwadayi da
soyayya, don zancen ya kasu biyu, ko dai qaunar mutum ko qaunar abin
abin hannunsa, in dai za a yi zancen qaunar mutum to ko kadan ba za a
duba cewa yana da hali ko bai da shi ba, bare a tambaye shi aikinsa da
irin gidan da zai zauna, da matsayin danginsa a gwamnatance, qauna tana
tsakanin zuciya ne da gabobi, ba ta qetare zuwa sutura ba bare a yi
maganar aljuhu.
.
In mutum zai nemi mace mai arziqi, to tun
farko kar ya yi zancen musayar motsin zuciya, ko ta yi masa hidimar yau
da kullum, bare kuma 'yan uwansa gami da iyaye, yana iya miqa wuyarsa in
bai da buqatar komai daga gare ta, a nan kuma ba mai iya kawo zancen
soyayya, haka ko shi namiji in dai za a gwamatse shi don abin hannunsa
shi kansa ya sani, zai yi wahala ya manta wahalhalun da ya yi kamin ya
mallake ta, to duk wanda bai wuce ga-shi ba, to lallai bai fi qarfin
wulaqanci ba, da yawa wasu sai dai su turo mata abubuwan sawwaqe rayuwa,
ko su ajiye saduwar dare a matsayin hanyar nuna soyayya, tabbas
wadannan sun yi hidimar badawa, amma zuciya ba ta yi aiki ba.
.
Daga yanzu za mu fara tunanin ko kallo daya zai iya sanyawa ka qaunaci
mutum, ka iya kasadar miqa masa rayuwarka har abada, ka ba shi amanar
jin dadinka na dindindin, da sakankancewa da cewa ba zai cutar da kai
ba, kuma ba zai yarda da duk wani abin da zai cutar da kai ba qarami ne
shi ko babba, ka tabbatar da cewa komai kake bida na duniya da shiriyar
lahira za ka iya samu a hannunsa, tabbas daga mace ta yi ado ba za a iya
gane hakan zai samu ba, haka daga namiji ya sami kudi ba zai yuwu a
sakar masa jiki ba.
.
Hanyoyin da za a bi don cin ma soyayya ta
gaskiya, da samun abokin rayuwa na qwarai, da juya tunanin masoyi gami
da toshe barakar da take fatattakar alaqoqin masoya da ma'aurata su ne
za su zama mana tafarki a wannan sabon shirin da yardar Allah...