baban manar alqasim..
Akwai wasu dalilai wadan da suke tunkudo
matashi zuwa ga soyayya, sai dai wasu ba su cika kula da su ba, bari dai
mu yi qoqarin lissafa su kamar haka:-
a) Qarancin tausasa wa
matashi a tsakanin uwaye yana ba da gagarumar gudummuwa wajen karkatatar
da shi zuwa ga inda yake zaton zai dan sami tausasawa, idan ya kasance
ba wani mai sakewa da shi, sai ya sami wanda zai zauna da shi na tsawon
lokaci, ya nuna masa cewa yana ma son ya kasance tare da shi kowani
lokaci, dole ya karkata inda hankalinsa zai kwanta, masamman yadda
halittar namiji take buqatar ta mace, ita ma ta macen take buqatar ta
namiji, in suka hadu sai soyayyar ta taqaitu wajen biyan abin da aka
rasa a baya, a maimakon saqa rayuwar da za ta dore har abada.
.
b) Karkata ta dabi'a wajen wani jinsi na daban sakamakon canjin da aka
samu na physiology ga matasa, matasanta a kowani lokaci ba ta kama da
yaranta, to ko yara ne akan sami irin wannan shaquwar ta buqatar wani
jinsi, a dazu na ji wani uba yana cewa: Uwar dansa ta roqe shi minti
guda daya ya hana ta, amma ya dauki jakar kacokan ya miqa wa wata
yarinya, matashi shi ya fi buqatar wani jinsi don sanyaya wa rayuwarsa.
.
c) Gasa a tsakanin matasa takan kawo kusantar jinsuna, sau da yawa wani
lokaci matasa in sun ga wata mace sukan taya wa junansu wanda zai iya
magana da ita, akan lura da aji, ko hasken fata, ko matsayi da dai
sauransu, saurayi bai son a ce duk tsararrakinsa suna da 'yammata sai
shi kadai, in ma shi bai nema ba abokansa za su matsa masa, a irin
wannan yanayi bai shirya kusantar wani jinsi ba amma rayuwa ta tilasta
shi.
.
d) Tasirantuwa da littafan soyayya, fima-fimai na
soyayyan da na batsa sukan sanya matashi ya buqaci wani jinsi wanda ba
na sa ba, galibin abubuwan da suke nunawa da wahala su faru a irin
wannan surar, yadda masoyi zai watsar da komai na rayuwarsa a kan wanda
yake qauna, har ya zama kamar bai da wani abin yi sama da buqatuwarsa da
masoyinsa, sai matashi ya fara tsammanin cewa shi ma in ya yi masoyi
haka za ta wakana, sai ya yi qoqarin jarrabawa, zai kuma buqaci soyayyar
ta yi daidai da wace yake karantawa ko yake gani, duk kuwa da cewar ko
su masu fima-fiman sukan sami matsala a rayuwar aurensu.
.
e)
Wani lokacin kuma matashi yakan yi zaton cewa yanzu fa ya girma, bai
kamata a ce babba kamarsa bai da budurwa ba, ko ita macen ta riqa jin
cewa ita ma fa ta girma, soyayya kuma ita take tantance girma da
yaranta, masamman wannan zamani na waya, da za ka ji ana magana ana
dararraku, wani lokaci a yi ta danne-danne ga waya, ana hira da budurwa
ko saurayi, za ka riski cewa wace ta girma ba matayi takan yi ta kuka
cikin dare, gami da salloli da roqon Allah, qaramar da ba saurayi kuma a
kira ta bera!
.
Soyayyar quruciya tana da tasirori da dama, da kuma abubuwan da suke alamta tunkudarta ga matashi, misali:-
a) Yawon da tunani yake yi wa matashi, galibi kwalliyar masoyi yake
tasowa a duk lokacin da matashi yake kadaita, kamar ni dai lallen da
mace take yi yana saye imani na, wani kuwa sam bai qaunarsa, yana da
abin da yake ba shi sha'awa, kuma zai riqa satar kallonsa a jikinta, duk
in ya kadaita sai ya riqa dawo da shi yana tunaninsa, ita ma budurwar
da abin da take kallo, tun ma ba ita ba, don tana iya bata komai a
dalilin wannan tunanin, wata qila ma ta rame kamar mai rashin lahiya.
.
b) Mafi yawan abin da yake tsakanin matasan buqatuwar juna ce, kowa
yana fatar a ce ga ranar da jikin masoyinsa zai halasta masa, don ya
jima yana kallon gabobin da suke motsa sha'awarsa, in da za su zauna yau
na tsawon lokaci, ba zai hana su buqaci zama nan gaba ba, don ba zaman
da buqatarsu take biya, kuma ba za su iya haqura da juna ba har sai
buqata ta biya, irinsa ne in ya zo da tsautsayi sai ka ga ciki ya bulla
wajen wace ba a taba zato ba, to soyayyar quruciya ta yi tasiri.
.
c) Sannu a hankali wannan soyayyar takan tashi daga mafarke-mafarkezuwa
buqatar kadaituwa da tunani, ta inda za ka ga matashi ya lumshe idanu
kamar yana barci, amma a farke yake, tsabar tunanin masoyi ce kawai ta
mamaye zuciyar, wani lokaci ma sai ka kira shi sau biyu kafin ya san
cewa da shi kake magana, da za a hana shi auren masoyin shi kenan wani
tashin hankali na masamman ya taso, ko mai karatu ne babu sauran zancen
imani da qaddara bare a sa rai zai yi haquri ya ci gaba da girmama na
gaba, matsalar tasirin soyayyar quruciya kenan da ta tattara a kan
sha'awa.
.
Masu bibiyarmu za su iya samun sauran shirye-shiryen a wannan rariyar ta qasa.