Wasu bama-bamai biyu da suka fashe a wani taron gangamin zaman lafiya a tsakiyar Ankara, babban birnin Turkiyya,y sun kashe mutane akalla 86.
Kimanin mutane 200 kuma sun samu raunuka.
Wani hoton bidiyo ya nuna masu taron gangamin sun rike hannayen juna suna maci tare da rera wakoki lokacin da bam din ya fashe.
A tashin hankalin da ya biyo baya, an yi ta jifar motocin 'yan sanda da duwatsu.
Gwamnatin ta yi Allah-wadai da harin wanda ta bayyana a matsayin aikin ta'addanci.
Amma shugaban jam'iyyar HDP mai goyon bayan Kurdawa ya dora laifin ne akan gwamnati.
An dai shirya gangamin zaman lafiyar ne domin a tilasta wa gwamnatin Turkiyyar ta daina kai ma sojin-sa-kan Kurdawa farmaki.