Mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya kawo
karshen jita-jitar da ake ta yadawa ta batun takararsa,
inda ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar shugaban
kasar a zaben da za a yi shekara mai zuwa.
Da yake magana tare da Shugaba Obama da kuma mai
dakinsa Jill a fadar White House, Mr Biden ya ce shi da
iyalinsa na makokin dansu ne da cutar Kansa ta kashe,
kuma ya tabbatar ba shi da lokacin yakin neman zaben
da zai kai ga nasarar tsayar da shi dan takarar
jam'iyyarsa ta Demokrat.
Ya ci gaba da cewa duk da cewa ba zai tsaya takarar ba
amma dai ba zai yi shiru a lokacin yakin neman zaban ba.
Masu aiko da rahotannin sun ce sanarwar ta sa zata sa
babbar 'yar takarar shugaban kasar ta Jam'iyyar
Demokrat din, Hillary Clinton, samun sa'ida.
Title :
Ba zan tsaya takara ba - Biden
Description : Mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya kawo karshen jita-jitar da ake ta yadawa ta batun takararsa, inda ya ce ba shi da niyyar ts...
Rating :
5