Bansan lokcin da wayar hannuna ta subucemin ba cikina ya fara juyawa na fadi qasa na fara rero kukan nadama...
Tabbas ni jahilace tana kuka tana surtai,banida ilimi gaskiyan ka deen
ni jahilace ina matar aure namaida wani namijin mijina ina xankai haqqin
aurene??
Kadan daga axabar da Allah xaimin kenan kamin inje qiyama inchi ubana...
Chikinta yaci gaba da juyawa, sai ta fara xubar da jini,
Ta tabbatar da idan har ciwo yakamata anan sai dai ta mutu ba wanda xaikaita asibiti,
Ta rarrafa tun tana ganuwa taja mota sai hospital, kamin ta Isa ta jiqe sharkaf da jini, bayanta kamar ya bude..
Takasa qarasawa cikin sai kwasarta akayi akayi ciki da ita,
Likitoci sukayo kanta, aka mata allurai....
Lokacinda ta farka taji ana qara mata ruwa, Dr yaxo yana mata sannu,
Hajia naziah sai dai kiyi haquri munyi iya bakin qoqarinmu na ganin mun
tsayar da xubar cikin amma abin yaci tura, qarke ma Sai mukaga idan
mukayi wasa xaki iya rasa rayuwar ki, sai kawai muka miki allura cikin
ya qarasa xubewa...
Wata hamdala tayi hadi da jin dadi, lallai Allah ya rufa mata asiri da ya xubar da cikinnan...,
Dr yace
Yanxu xamu baki allurai da yan magunna kuma yakamata ki sanar da mai gidanki halin da ake ciki, kamin mu sallameki,
No Dr maigidana baya gari kuma ni ba yar nan bace.! Tafada muryanta yana hadewa,
Dr ya kalleta yace to shikenan xaki xauna anan har zuwa gobe ko jibi idan kin qara Samun lafiya Sai mu sallameki...
Dr kayi haquri ka sallameni yanxu kaga banxo da phone dina ba kuma
nasan mijina da iyayena xasuyi ta nemana hankakin Su xai tashi ataimaka
min please Dr...!!
Hajiya baxai yiWu ba, duk da kinada cikakkaiyar lafiya amma ya dace kidan
Samu rest, duk yanda Dr yayi akan naziah ta bari har gobe idan taqara
jin sauqu a sallameta ta tafi gida amma abin yaci tura, ta nace akan
tunda tanada lafiyar ta gida xata tafi...
Ya rubuta mata magunguna
da kuma allurai , kuma yace tana buqatar hutu da natsuwa, yace mata
mahaifarta ta sami matsala xata riqa zuwa ana dubata har ta Sami
lafiya,kuma idan tayi wasa xata iya rasa haihuwa har abada, ya qara bata
haquri akan Kasa war da yayi na ceton yaron dake cikinta kamar yanda ya
mata alqawari anan dai ya qara mata bayanin cewa dama cikin xai xube
dan ba daidai yakeba, haka ta dawo gida guraren 11 na safe, tanata saqe
Saqe aranta har ta iso gida,
Nidai banyi dacen rayuwa ba, na cutar
da kaina na cutar da mijin aurena, nakasa kare darajar aurena, qarke ga
yanda deen dina yamin, Lallai maxa ba abin amince wa bane, anya kuwa
deen dinane yamin haka??
Dayan xuciyar ta ya bata Amsa Eh deen dinke malam naziah...
Any how mun tashi 1__0, tasha alwashin sai ta rama abinda ya mata...
"Kinji hauka ko ina xata Ganshi ta rama ohoooo"
Ta iso gida ba qarfin jiki, ta Samu tayi wanka da ruwan dimi ta qasa
jikinta Sosai tasha tea ta nemi guri ta kwanta, a baccin ma dai mafarkin
deen ta riqayi, tana taShi ta tsine ma baccin da mafarkin gaba daya..
guraren qarfe hudu na yamma sms ya shigota, taji duuum nurane
"JIBI NIHAL XATAXO KI GYARA MATA DAKINDA XATA SAUKA" ....
Tayi duum ita kadama suxo Suga halinda take ciki su ganota,
Hakanan ta lallaba taje dayan banqaren ta dan gyara sama sama, ta koma dakinta, dama naziah akwai xama daki
Yauce ranar da nihal xata iso guraren 4:pm xata iso,
Nura yasa an yo siyayyah abubuwa kala kala duk na tarbar nihal,
Naziah aranta taji tana son gani wannan yarinyar da ake axarbarbabin zuwanta...
kamin qarfe biyu ta kammala hada komai gida yayi fes dama fes yake
girki kala kala ta hada duk na tarbon nihal, itama dai tadanyi wanka duk
da yanayin yanda ta kode ta chanxa tayi wani iri da ita amma dai tayi
kyau, abinka da kyakyawan mutum...
Tana xaune parlour tana kallo har
guraren biyar basu isoba,lokacin shan maganinta yayi ta shiga daki
kenan taji qarar mota haka qirjinta ya riqa dukan uku uku, ko miye haka
ohoo..!!, tanajin maganar Su sama sama, abinda yafi bata mamaki muryar
wacce takeji kamar tasan muryar amma ta manta inda tasan muryar,
Aunty..!
Aunty..!!
Auntyyyyyyy..!!!
Ina kike gamu mun iso, muryar da taji kenan ana gwalla mata kira,
Shikam nura yana ijiye nihal ya fita dan kada naziah ta kwafsamai gaban m nihal....
Na'am ina zuwa... naziah ta bada amsa a taqaice..
Ta fito qamshin da taji Lallai tasan qamshin, amma tasan hancin tane yake yaudararta...
Tafito da Walwala abinda take gani gabanta yafi bata mamaki akan komai,
ba kowa bace face tsahuwar qawarta da tafi tsana a rayuwar ta itada
mugun uncle dinta wacce Sanadiyar su ta bata wato sista khadee, tuni ko
wacce ta daure fuska naziah ta kalli s...khade a wula qance ina nihal
take??
Nihal ta kalli naziah cike da mamaki da al'ajabi Lallai
wannan naziah ce kuma itace matar uncle dina dama ance mata sunanta
naziah...!!
Kuuut yau ake yinta..
Ko wacce na kallon yar uwar
ta, nihal cike da mamaki tace nicefa nihal din,naziah tace miya kawoki
nan gidan, suna cikin magana kawai sai ga nura ya shigo...
Nihal..!!
Nihal...!!
Ya Shigo da kaya niqi niqi a hannu yana kwalawa nihal kira..
Abinda ya gani shine ya bashi mamaki hade da daure kai, ledodin hannun sa duk suka xube,
Jikin Sa na rawa hadi da sarqe war murya ta tashin hankali hadi da
tsori ya kalleta murya na dancing, ke miyaa miyaa kawoku gidanaaa.!!??
kinxo dan ki tarwa tsamin iyali na hadi da jin dadina ko??, waima uban
wa ya baki address din gidana...!!! Naziah ta gama raxana jin yace miya
kawota gidan sa, idan dai nan gidan sane to Lallai mijintane!!
Kuma shine uncle din sista khadee da yace mata almajira kuma ya mareta, shine mutun na farko data tsana a tarahin rayuwar ta.!!
Shine sanadiyar batanta.!!
Kuma shine mutumin da ta qara tsana second time a rayuwarta wanda yayi sanadin shiga tashin hankalinta..!!
Jin tayi an katsata da wata irin tsawa ke hulwa badake nake magana ba??
Nura ya kalli nihal yace ke ina naziah ta shigane??
Nihal ta kallu uncle dinta cike da mamaki tace uncle wannan ma ai sunanta kenan fa naziah .
What???
Eh uncle itama sunanta nazia....
itace qawata da nake baka labari lokacin,
kuma itace wacce ta maka rashin kunya lokacin da taje gidan mu,
No bashi nake neman saniba nihal.! wai itace matar tawa???
nihal da mamaki ta kalli uncle dinta.! tace kaman ya uncle dama bakasan matar taka ba???
yayi shiru yarasa abinda xai fada...
ita nihal mamakinta shine wata hudu dayin auren baima tama sanin matar
ba to ya akayi akace mata tayi ciki?? kuma uncle yace mata bai santaba
baima taba ganintaba amma batayi tunanin abin yakai hakaba!!!
nazia
iya tunaninta ta gane cewa lallai wannan nura shine mijinta, kuma shine
uncle din sis khadee, kuma shine deen dinda ya yaudareta yaci mata
mutunci....
Dukansu sunyi churko churko kowa ya rasa abinda xai fada.!!
nazia taji tsoro matuqa tayi tunanin kada su mata wulaqancin dayafi
wanda deen ya mata da wanda wannan tsohuwar qawar tata ta mata, tajuya
xata koma dakinta ta tattaro kayanta ta wuce gida tunda dama ya saketa..
tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki dama batada lafiya cikinta daya xube...
tayi taku biyu uku kikajita lauuuuu... ta fadi "nima abdool bansan miya
sa ta fadiba" duk sukayo kanta nura jikinsa na rawa yake bubbugata amma
ko motsi batayiba hankalinsa ya tashi matuqa suka yayyafa mata ruwa
amma inaaa shiru da sukaga xasu bata lokaci sai suka dauket
sai asibiti....
a hanyar asibiti kamin a isa ta farfado taganta a mota tayi yunqurin
miqewa xaune taji an dan daneta irin ta kwanta dinnan a jikin wani
qamshin da takeji yana dukan hancintane ya tabbatar mata cewa tana tare
da deen ne ta daqo dagyar tana dubawa taganta ashe jikin deenma take
kwance...
dukda rashin qarfin jikintanba bai hanata tashi a jikinsa
da qarfiba hadi da dalla mai harara da wani uban tsakiba, ko ajikinsa
shidai ta samu lafiya itada dan cikin da ke jikinta!!! "kunji wawa baima
san cikin ya xubeba koni abdool da masu karatu munsan cikin ya xube ko
baku saniba��??"
kusaukeni anan.. !! ta fada a taqaice dan bata iya magana sosai. deen ya bude baki xaiyi magana...
Nace a saukeni anan!! Wannan karo da gadara hadi da isa ta fada tare da tsiwa irin tata,
komai ta fanjama fanjam...
ta murda marfin motar wallahi idan baku tsaya ba xan sauka, kuma motar tana tafiya ne...
deen ya tabbatar da xata aika yacema nihal ta tsaya tafita ta basu wuri...
nazia tamai kallon banxa. dawa xa'abarka???
Ya kalleta ya marairaice haba hul....
ta katseshi da sheeeeee....!!!
yimin shiru munafuki macucu mayaudari lokaci daya ta kirashi da sunayen ta bude marfin motar da qarfi ta fita abinta...
yafito yabita a baya har xata shiga taxi yaja ya tsaya yabita da kallo
hadi da kallon cikinta lokaci daya Allah ya sakamar qaunar cikinta fiye
da yanda yake tunani...
nihal nason tayi magana amma kuma yanda taga ya daure fuska ya wani chanxa sai tayi shiru...
chan kuma sun kama hanya tace uncle nifa bangane wannan abunba nakuba naga..
bakuma xaki ganeba...
ya bata amsa a taqaice, ta kalleshi ta gefe, har xata qara magana ya katseta..
kuma banason inji wannan abinda ya faru gurin kowa...!!
hmmmm..! nihal taci gaba da driving dinta,
uncle ina xamu tafi yanxu..
gidana!!
nanma amsar a taqaice ya bata..
To ai..
to ai me? look nihal kindameni da magana kibarni inji abinda nakeje pleaseeeeeeeee...! har suka isa bata qara mai maganaba...
nazia direct gidan su ta wuce tana xuwa ta fada jikin innarta tana kuka,
inna tana tambayarta abinda ya faru dagyar ta iya bude baki tace nurane ya sakeni .!!!
Inna tasaka salati..! sakifa kikace!!! eh wallahi inna ya sakeni!!
inna tana ganin abin kamar bada gaskeba ko kuma mafarki,
to Ina takarda, nazia tadan taqaita kukan nata tace takarda tana gida namanta da ita, hankalin inna inyayi dubu ya tashi,
inna ta kalleta rai a bace kinga yanda kika dawo lokaci daya kamar mai jego!!?
qirjin nazia ya qara bugawa..
waima miya hadaku ne da har ya sakeki??
naci gaba da kukana ban bata amsaba inajinta tayi waya da yaya ta gaya mar abinda yake faruwa.
bansan abinda yace mataba kawai sai naji tace to sai ka iso ta kashe wayar...
taxo taxauna kusa dani, tayi tagumi chan kuma tace,
Allah dai ya saukeki lafiya amma wallahi yaronan baiyi halin iyayensaba, amma dai bari muji miya hadaku kamin ince wani abu. !!
Wani rasss naji dama inna tasan inada ciki kenan ?? to ya akayi suka gane inada ciki?
yanxu idan ma nace baitaba kusantanaba ba yarda xasuyiba
Lallai da sake dole insan yanda xan bulloma lamarin "xancen xuci takeyi" Allah nagode ma da ka xubar da cikinnan..
na tashi xan shiga dakin inna kenan, sai sallamar yaya mukaji yashigi
kamar an turo shi yayi jaaa kamar qauta�� sai huci yake kamar wani
kasa...
wallahi inna tun farko nasan xa'ayi haka.!! nurr bayason
nazia itama bata sonsa amma muka rufe ido muka ce sai anyi auren nan
kuma na gaya miki haka tun farko yanxu ga wulaqancin da yayi mana nan
yasokota dan ma cikarshi dan iska baitashi sakintaba saida ya mata ciki
yanxu dan Allah inna abinda yayi ya kyauta kenan??
Ya mata adalci kenan??
yanxu ki.....
inna ta katseshi kai wai wane irin mutunne kai bakasan miye ya hadasuba
kawai xakaxo kana ma mutane rigimar banxa, Ai ka bari ta mana bayanin
miye ya hadasu har ya saketa sannan ka fara rigama rigimamme kawai.!
dan taxo tace yasaketa haka kawai ba fada ba komai xai saketa?? dukansu
basason juna to katabbata akwai laifin kowanne su aciki kabari tayi
bayani da bakinta, ta kuma nuna takardar sakin sai aji yanda xa'abullowa
abin..
yaya yayi ajiyar xuciya ya nemi guri ya xauna, amma fuskar nan har yanxu a turnuqe,
ya kalleni cike da tausayi kiyi haquri nazia kidaina kuka Allah xai saka miki idan ya yaudareki ina takardar sakin naki,??
Nazia ta bude baki dagyar muryanta duk ya dushe..
yana gidan!
miyasa bakixo dashiba,
mantawa nayi dashi.
gobe xamuje ki dauko kayanki da kuma takardar Allah ya sakamiki!!, ana
cewa ya natsu ashe da sauransa, ni da ganin idinsa nasan baida kirki
mutum banxa ay dama nasan xaiyi fiye da haka....!!
Inna ta kalleshi rai a bace waikai lafiyanka?
waya gayamaka ana shiga tsakajin mata da miji.?? wallahi xasu baka kunya daga baya ana ma magana kamaida ni mutuniyar banxa...!
ai inna duk ke kika janyo tun farko ni banso auren nan ba amma kika
nace sai anyi sannan yanxu ga wulaqncinda yaI mata kina cewa abari sai
anga takarda, kawai inna kisa mana ido dan ba qara bari xamuyi mu
maimaita kuskuren farkoba dole in nemawa qanwata yanci dan anga bamuda
uba..!!
Karo na farko da yaya yaqi sauraren inna idan tana magana, haka idan tana magana ya maida mata amsa..
mamakin duniya yacika inna tasaki baki sululu tana kallonsa,
Lallai baitaba mata hakaba, kawai bari ta barshi
har ya sauko sannan suyi magana su fahimci juna.
ya tashi fauuuu... har yakai qofar fita ya juyo ke nazia xo muje,
na kalli inna naga ta dauke mana kai na fuske abina nabi yaya ina dan dingishina.
part din yaya muka wuce da yake an gyarashi tunda yaya ya kusa aure da zainb khalifa.!
mukaje sashensa muka xauna a parlour yaya yaso yamin magana amma ganin
fuskata yanda na harqitse yasa yaja bakinsa ya dinke, amma ransa a bace,
ki shiga dakina ki kwanta ni xan kwana anan kamin gobe muga yanda xa'ayi..
ba musu na amince dan bayana kamar ya bude dan xafi gashi na jiqe sharaf da jini, ina buqatar xagayawa in kimtsa jikina...
na tashi naje dakinsa..
direct bayi na wuce dan in gyara jikina saidai kuma ba pad sai da tissue nayi amfani na watsa ruwa na fito..
ina fitowa na nemi guri na baje.
abinka da mara lafiya ga gajiya nandanan bacci yayi awon gaba dani...
A bangarennura ko kuma muce deen,
ya gama rudewa ya zare kamar wani dan qwaya..
dama hulwarsace matarsa??
dama itace a gidansa bai saniba??
yanxu tana dauke da cikinsa!
waima ya xaman cikin yake shege ko mai uba.!??
dana ba shege bane!
dana dan halal ne koda bada sanin junan mu muka sameshiba.! dayan bangaren xuciyarshi ya bashi amsa,
ina qaunar dana fiye da raina!
lokaci daya qirjinsa yayi wani mummunan bugawa daya tuna cewa ya saketa!!
ya tuna wulaqancin da yamata. anya xata yafemin kuwa??
bangaren xuciyarshi ya bashi amsa da xata yafe masa tunda tana sonsa!!
amma yana tunanin baxata taba yafe marba.....
yafi yarda da cewa baxata yafemar ba.
kuka ya saki kamar qaramin yaro ya durqushe qasa lallai na yaudari kaina na yaudari soyayyar da hulwaty
ta nunamin, ya rasa yanda xai yi da rayuwarsa, xuciyansa kamar ta fito
dan baqin ciki da damuwa babban burinsa ta isa gida lafiya..!
waima
da wane ido xai kalli iyayenta dama nashi iyaye iyayenta sun mai
karamci tun tana jinjira ya nemi a bashi ita kuma aka bashi aka
ijiyemasa ita tun lokacin har ta isa aure lallai ya xalunceta, koda baya
sonta baidace ya mata abinda ya mataba, kodan karamcin da iyayen ta
suka mai , mixaicewa iyayensa idan sukaji cewa ya saketa.!?
yanxu
yake tuna maman nihal ta taba cemar nazia nada cikii yana kallonsu wani
iri har yake ce musu shi ko ganinta yayi baxai ganeta, ashe da gaske
hulwarsa tana dauke da cikinsa..!!
Lallai ya tsuke tunaninsa ya
akayi bai ganetaba? ya akayi bai gane sunantaba..!? Ta taba gayamin
sunanta nazia amma tace babanta yana kiranta da hulwa, so tafison
sunan shi yasa bai gane sunanta na asali ba.
ya tuna lokacinda xai siyamata ticket daga abuja xuwa sokoto yaga sunanta Nazia muhammad amma baiganetaba.!
duk tunanin daya dauko baya kaiwa qarshensa, yaga ba yanda xa'ayi ya ganeta, amma hadda jahilci yayi mai yawa .
yanxu yatuna ya kirata hulwarsa da jahila ashe nine jahilin nine
daqiqin nine axxalumin yaci gaba da kuka hadda gunji kamar qaramin
yaro....
nihal tana parlour tayi jigum tajiyo kamar ana kuka ta leqo taga lallai uncle dintane yake kuka..!!
itakam ta rasa gane komai duk tunaninta bata samun amsa, lokacinda xata
iso Mamanta tace kada ta riqa barin antin nata da aiki dan tanada juna
biyu (ciki)
lokacin da taxo uncle da aunty nazia sun nuna basu ma san juna ba.!!
duk tunanin ta bata sami amsaba.
taja ta tsaya qofar dakinsa. tana tsoron ta shiga dakin ya balbaleta da masifa gashi ya gargadeta..
ganin kukan da yake ya tsananta da wani gunji da yake yasa bata tsaya wata wataba ta fada dakin taje gunsa cikin tsoro,
uncle miyake faruwa??
kamar baijitaba
ta qara maimaita tambayar har saida ta tabashi da qarfi sannan ya dago
ya kalleta yanda taga ya chanxa ya hargitse lokaci daya abin ya bata
mamaki da tsoro..
kodai yanada aljanune??
ta kalleshi uncle mi yake faruwa ??
ya kasa magana amma dai ya daina kukan da yakeyi,
ya dago ya kalleta abin tausayi dashi " koda niabdool bancika jin
tausayin maxa mayaudaraba ba dan basuda kirki amma yadan bani tausayi
kadan" ya bude baki nihal xaki timakeni???.
Eh uncle xan taimakeka..!!
kinyi alqawari!??
Eh nayi..!
Duk wahala???
Eh.!!
nihal talk tome ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali kimin
alqawari idan kowa ya gujeni ke xaki tsaya tare dani xaki rufamin
asiri..!!?
Uncle na maka alqawari duk wuya duk wahala xan kasance tare dakai har qarshen rayuwata...!!!
Yaji dadin alqawarin da nihal ta daukar masa yasan kuma akwai ta da
jajircewa akan abinda takeso idan har ba wulaqanci a ciki. ta yarda
dashi saidai tunaninsa daya ya xasu bullowa abin., ? Dolene ya gayawa
nihal gaskiyar abinda ya faru anya zai iya kuwa? tabbas baxai iyaba zai
tonawa kansu asirine kawai wannab sirrine tsakaninsu baidace kowa
yajiba. zaidai san yanda zai bullowa abin. Nihal dai tana zaune tana
kallon uncle dinta duk da ya daina kuka amma yana wani gunguni gunguni
dukkan alamu dai ya zautu ta kira sunansa uncle ya dago ya kalleta, au
kinanan? Ai
Kina iya tafiya, tace to, ta tashi ta tafi cike da saqe
saqe a ranta haka yaci gaba da tunane tunanensa yana kuka har barci
yayi awon gaba dashi..
Bai farka ba sai guraren asuba ya tashi
idonsa sunyi hulu hulu ba kyan gani. Maimakon yayi sallah sai ya wuce
dakin hulwarsa yana shiga ya dauki turarenta yana shinshinawa hadi da
hugging din kwalbar turaren yana kwalla kamar wani xararre ya tashi
yana yan tabe tabe tabensa har yakai gun wayarta battery low ta mutu ya
jona chaji komi yake nema oho ya dauko hand bag tinda yana lakube anan
yayi karo da takardar sakinta da magungunab.! vai duba maganin kona miye
ba tunda yasan tanada ciki xai xama maganin masu cikine. Aranshi Wato
bata tafi da takardar ba "yama manta da cewa suma tayi a hanyar hosptl
ta farfado tace a kaita gida" lokaci daya baqin cikinsa ya dawo farin
ciki yayi wani murmushi bada bata lokaciba ya shiga bayinta ya yayyaga
takardar yayi xuba a bayi yayi bayan gida akai�� ya kora rowa yayo
alwula yaje yayi sallah... Allah kadai yasan abinda yake saqawa a ranshi
har gari ya waye yana laximi akan Allah yasa ta yafe masa su dawo
normal...
Yaxo ya sami nihal ta hada mai break fast bai iya ci sosai
ba yadan taba dai kawai duk dahaka nihal tayi mamakin sakewar da yayi
akan jiya. Nan xarginta ya qara tabbata akan uncle dinta yanada jinnu
dan su suke haka one time kuma kamar ba'ayiba
Taso suyi magana sai kuma ta basar tunda jinnu ne baxai tuna komai ba....!!
Naxia bata farka ba sai guraren 8 na safe duk jikinta ya qara ciwo
sabida batasamu tasha maganiba, ta rarrafo taxo palo ta sami yayan ta
bayanan tasan ba gurin aiki yaje ba dan sai 10 yake tafiya aiki?, tayi
tunanin bari taje kitchen ta hada tea ta kora tana xuwa taga yayanta
tana fere dankali abin ya bata dariya dan bata taba ganin yaya a
kitchen ba. duk ya xubar da rabi garin ferewar aranta tace lallai zainb
khalifa xatayi fama ko irin mata bataji dadiba miji ya tayata girki da
dan ayuka yaya kam ba abinda xai tabuka. Ta kalleshi ta gaidashi ya amsa
cike da fara'arsa hadi da tausayin yar marainiyar qanwarsa!!! kin
tashi tace eh.! Ka kawo In qarasa yace aah ki barshi xan qarasa kina
baquwar tawa sukayi dariya... AI yaya a wannan duk ka xubar da rabin
dankalin yayi murmushi ina practice ne kamin maaadam taxo dariya ta
kamani amma na fuske wato zainb khalifa ce maaadam. lallai rayuwa mai
juyi da yanda yaya ya tsani xainb khalifa amma yanxu itace wacce yake
burin ta xama uwar yayansa....
Kije ki shirya muje gidan wancan yaro ki dauko takardar sakinki da kayan buqatarki.
No yaya muje a haka kayana duk suna chan gidan.
Kije ki duba wardrobe dina zaki ga kaya ki xabi daya ki saka
Naje dakin abin ya bani mamaki ganin kayan mata kamar wani qaramin
store ta dauki wani dogon riga baqi ta saka duk da ta rame amma kayan
su. Karbeta sosai.
Koda ta fito harya qare hada musu break fast ta xauna suka ci lallai taji yunwa rabonta da abinci tun jiya da safee.!!
Suka fito sukaje sashen inna suka gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa
suka gaya mata zasuje gida nura in dauko takardar sakinna da kayana har
sunkai bakin qofa inna tace ban yarda kuyi chin mutunci da kowaba yaya
ya amsa da insha Allah..!