Shugabannin jam'iyyar APC suna zargin an yi
masu sauki dora akan zaben wanda zai zama
minista daga jihar.
Alhaji Ahmed Lawal
sakataren tsare-tsare na jam'iyyar a jihar ya
bayyana dalilansu na wannan korafin da suke yi.
A cewarsa ba'a tuntubesu ba a jam'iyyance kafin a
zabi wanda aka fitar da sunansa.Yace ya kamata
duk abun da za'a yi a nemi shawarar jam'iyya.
Idan za'a bada mukami yakamata a dubi wadanda
suka yiwa jam'iyyar fafutika har ta kaiga kafa
gwamnati.
Alhaji Ahmed Lawal yace wanda aka dauko a ba
minista su har ga Allah basu sanshi ba. Ba mutane
wadanda basu yiwa jam'iyya komi ba mukami shi
zai kawowa jam'iyyar matsala a zaben 2019 mai
zuwa, inji Alhaji Lawal.
Shi ma wani kusa a jam'iyyar Dr. Umar Duhu
tsohon shugaban jam'iyyar a yankin arewa maso
gabas yace akwai bukatar a sake nazari akan
ministan da aka dauko daga jihar Adamawa.
Yakamata a yi tafiya tare domin zabe mai zuwa.
Idan ba'a yi ba su 'yan siyasa zasu koma gefe daya
suna kallo. Kafin a yi nisa ya dace shugaba Buhari
ya yi gyara domin Muhammad Bello da ya dauko
daga jihar Adamawa ba dan siyasa ba ne.
To saidai 'yan tsohuwar hukumar alhazan jihar
Adamawa daga inda aka zakulo Muhammad Bello
sun yabawa shugaba Buhari da zabarsa. Alhaji
Aminu Iyawa tsohon kwamishana a zamanin
mulkin Nyako yace zaben Muhammad Bello ba sai
an tuntubesu ba saboda ya dace. Yace shugaba
Buhari ya ba dan siyasa daga jihar mukamin
sakataren gwamnati saboda haka ba jihar
mukamin minista kuma kamar garabasa ce.