Ma'aikatan kafofin yada labarai da manazarta a
cibiyoyin bincike da jami'o'i da marubuta
littattafai da kuma daliban kimiyar harsuna suka
halarci taron.
Mahalartan taron sun fito ne
daga ciki da wajen Najeriya.
Dr Yakubu Magaji Azare shugaban kwamitin
shirya taron ya bayyana makasudin taron.
Yace shekaru da dama ana gudanar da fasara a
kafofin yada labarai da kotunan shari'a da
majalisun dokoki da ma hukumomi masu zaman
kansu domin isar da wani sako. Yace an fahimci
cewa ana yawan samun kurakurai ko kuma rashin
daidaito wajen yadda ake gabatar da fasare
fasare.
A wasu lokutan ma akan samu wadansu da basu
cancanta a ce sun shiga cikin yin fasara ba. Amma
suna yi mata kutse suna shiganta da ka.
Masana da shehunnan malamai su ne suka gabatar
da makaloli kan dabarun aikin fasara da tafinta.
Batun sabuwar figa ko fasahar fasara ta kafar
internet da ake kira google translate ita ce
makalar Farfasa Salisu Yakasai na sashen koyarda
harsunan Najeriya a jami'ar Usmanu Dan Fodio
dake Sokoto.
Farfasa Yakasai yace yanzu likkafar Hausa ta yi
gaba domin ta samu shiga cikin rukunin tsari na
fasara. Da an buga za'a samu fasara na kalmomi
har da wasu bayanai ko juloli. Wannan sabuwar
fasaha ta zauna daram ko ana so ko ba'a so.
Wata ba'amarikiya da ke nazari akan harshen
Hausa da ta halarci taron tace tana da sha'awar
fasara daga Hausa zuwa Turanci sabilin
kasancewarta ke nan a wurin taron. Idan akwai
kungiyar fasara zata iya bata fasararta a duba
mata.
Malam Ado Ahmed Gidan Dabino wani
shahararren marubucin littafan Hausa yace fasare
fasaren baya tun daga Abubakar Iman yanzu sun
banbanta. Yakamata a kawo daidaito da abun da
ya faru jiya da yau.